A ranar Lahadi ce wani hoto ya karade gari a shafukan sada zumunta da ke nuna Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi tare da Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, tare da wasu buhuna a tsakaninsu.
Masu amfani da shafukan dai, musamman Facebook da Twitter sun yi ta tsokacin cewa kudi ne a cikin buhunan Ministan ya kai wa shugaban jam’iyyar.
Bayanai na nuni da cewa an dauki hoton ne lokacin da Amaechi ya ziyarci Abdullahi Adamu a gidansa da ke Keffi a Jihar Nasarawa a karshen mako.
Alal misali, wani mai suna T’Challa a shafin Twitter ya ce, “Kun ga tilin basukan da Buhari da Amaechi suka rika ciyowa daga China a cikin buhunan nan guda uku ko?”
“Ku kalli Amaechi da ya ce ba ya son kudi. Ga shi nan buhunan kudin ne a tsakaninsu da Amaechin ya kai wa Shugaban APC,” inji wani mai suna Ogochukwu, a shafinsa na Twitter.
Abin da muka gano
Aminiya ta gano cewa gaskiya ne Amaechi, wanda ke neman takarar kujerar Shugaban Kasa a APC, ya ziyarci gidan Shugaban jam’iyyar a Keffi ranar Lahadi.
Ana ganin ziyarar ba za ta rasa nasaba da tuntubar da Ministan ke yi ta neman takara a zaben 2023 mai zuwa ba.
Sai dai ba mu iya tabbatar da cewa Amaechi ne ya zo da buhunan ba, ko kuma kudi ne a cikinsu.
‘Bai shiga gidan da buhunan ba’
Wata mai suna Habeebah Suleiman, wacce ta ce tana cikin tawagar Ministan yayin ziyarar ta tabbatar da cewa sun gana, amma Amaechi bai wuce minti 20 a gidan ba, kuma sam bai je da tsabar kudi ba.
A wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, Habeebah ta ce, “Sam babu adalci. Ina wajen jiya [Asabar] a Keffi, gidan Shugaban APC. Lokacin da Amaechi ya shiga, ko minti 20 bai yi ba, ya fice.
“Ko da jami’in tsaro daya bai shiga ciki ba, ballantana buhunan ‘Ghana Must Go’, kai ko ma jakar hannu bai shiga da ita ba” inji ta.
Sai dai binciken da muka yi ta manhajar tantance hoto ta Google Reverse Image Search, bai nuna ainihin wajen da aka dauki hoton ba, saboda haka ba za a iya tabbatar da ko hoton sahihi ba ne ko kuma jirkita shi aka yi.
Bugu da kari, hoton ba ya cikin wanda jam’iyyar ta fitar bayan ziyarar Ministan.
Da Aminiya ta tuntubi wani jami’in jam’iyyar APC da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana hoton a matsayin hayaniyar masu amfani da shafukan sada zumuntar, inda ya ce babu komai a cikinsa sai shiririta.
Gaskiyar lamari
Ko da yake an ga buhunan na Ghana Must Go a tsakaninsu a hoton, babu wata hujja da ke tabbatar da cewa Ministan kuma dan takarar Shugaban Kasar ya kai wa Shugaban jam’iyyar kudade.