✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakalar Kudin Fansho: Ina fama da matsananciyar rashin lafiya —Maina

Yana da hakki a matsayinsa na dan kasa ya yi rayuwa da cikakkiyar lafiya.

Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Gyaran Fansho ta Kasa (PRTT), Abdulrasheed Maina ya ce yana bukatar agajin gaggawa, sakamakon matsananciyar rashin lafiyar da yake fama da ita.

Maina, wanda yanzu haka ke tsare a gidan yarin Kuje, ya bayyana hakan cikin kunshin bukatar da lauyansa Ibrahim Idris ya shigar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Maina ya roki kotun da ta ba da umarnin wucin gadi ga Ministan Harkokin Cikin Gida da Babban Kwamturola na Kasa hadi da Alkalin Alkalai, da su gaggauta kai shi Babban Asibiti domin jinyar cutar da ke barazana ga rayuwarsa.

Haka zalika, lauyansa ya roki kotun ta duba wannan bukatar, kasancewar Mainan na cikin mawuyacin hali da ke bakatar gaggauta duba lafiyarsa.

“Yana da hakki a matsayinsa na dan kasa ya yi rayuwa da cikakkiyar lafiya da mutuncinsa, sai dai yanzu wadannan abubuwan duka na fuskantar babban kalubale,” a cewar lauyan.

A zaman da aka yi na ranar Talata, Alkalin Kotun, Inyang Ekwo ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Oktoba.

Tun a ranar 8 ga watan Nuwamban 2021 ne Alkali Okon Abang na Babbar Kotun Tarayyar ya yanke wa Maina hukuncin daurin shekaru takwas a gidan yari, bayan samunsa da laifin karkatar da kudaden fansho har Naira Biliyan Biyu, lokacin da yake shugabantar PRTT.