✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakalar kudi a FCE Zariya ta rutsa da dalibai 1,210

dalibai 1,210 na Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya (FCE) da ke Zariya, ba su san makomarsu ba, sakamakon biyan kudin makaranta da suka yi a…

dalibai 1,210 na Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya (FCE) da ke Zariya, ba su san makomarsu ba, sakamakon biyan kudin makaranta da suka yi a asusun ’yan damfara.
A yayin da Aminiya ta tuntubi Magatakarda da Ma’ajin Makarantar, Dokta Jibril Lawal da Alhaji Sani Uwais, sun tabbatar da aukuwar wannan al’amari.
Alhaji Uwais ya ce: “Eh da gaske ne dalibai 1,128 da kuma karin 82 wadanda aka gano daga baya sun biya kudin makarantarsu a wani asusun banki, wanda ba na makarantar ba. Muna da asusun banki na bai-daya, wanda ke Babban Bankin Najeriya (CBN). Duk wani biyan kudi, a wancan asusu ake yi. Amma bincike ya nuna cewa wadannan dalibai ba a wannan asusu suka biya kudin makarantarsu ba. Wannan shi ne abin da muka gano zuwa yanzu. In akwai wani karin bayani, za mu sanar da jama’a.”
A wani gefen kuma, wata majiya mai tushe ta zargi wadansu daga cikin manyan jami’an kwalejin da hannu a cikin wannan badakala. Majiyar ta ce kudin da suka hallaka na daliban sun kai kimanin Naira miliyan 29. “Akwai dalilan da suke nuna cewa wadansu daga cikin shugabannin wannan makaranta na da hannu a cikin wannan badakala. Babu yadda za a yi wannan al’amari ya faru ba tare da sa hannun manyan jami’an makarantar ba. Don haka muka rubuta koke zuwa wajen ’yan sanda. A yanzu daya daga cikin jami’an makarantar ne ke shugabantar binciken. Wannan ba adalci ba ne. Gwanatin Tarayya ya kamata ta nada kwamitin bincike don gano gaskiya. Babu gaskiya in aka ce mutumin da ake zargi ya zama alkali a kan abin da ake zarginsa,” inji majiyar Aminiya.
Da wakilinmu ya tuntubi  Kakakin Rundunar ’Yan sandan  Jihar Kaduna, ASP Aliyu Usman, ya tabbatar da cewa rundunar ta karbi takardar koke daga wadanda abin ya shafa. Jami’in ya ce rundunar ta fara bincike a kan lamarin.
Wata majiya mai tushe ta ’yan sanda ta shaida wa Aminiya cewa rundunar ta riga ta gayyaci wadansu daga cikin manyan jami’an kwalejin. Majiyar ta yi zargin cewa akwai masu kokarin ganin an kashe maganar ba tare da an ba wadannan dalibai hakkinsu ba.
Wadansu daga cikin iyayen daliban da Aminiya ta tuntuba sun yi kira ne ga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da ta sa baki wajen binciko gaskiyar abin da ya faru. “Kowa dai ya san halin da ake ciki a wannan kasa a yanzu. Da kyar na samu kudin da na ba ’yata don ta biya kudin makarantar. Sai da na yi wata uku ina tari kafin in hada kudin. Yanzu a ina zan samu wasu kudin? Muna kira ga gwamnati ta sa baki domin makarantar ta biya mu kudinmu, tunda su ne suka ba da lambar asusun bankin da ’ya’yanmu suka sa kudin, ta yaya kuma za su ce mana kudin ba su shiga ba?” kamar yadda wani daga cikin iyayen yaran ya ce.