Hukumar da Yaki da Ayyukan Zamba (ICPC) na neman surikan Shugaba Buhari, Gimba Kumo kan badakalar Dala miliyan 65.
Sanarwa da kakakin ICPC, Azuka Ogugua, ya fitar ta bukaci jama’a da su taimaka mata da bayanai da za su kai ga gano inda mutanen da take nema ciki har da surikin na Buhari suke, ko kuma su sanar da ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.
- Kwastam sun kashe mutum 5 a garin kama shinkafa
- Hotunan Sallar Idi daga Fadar Shugaban Kasa
- Ramadan: Darussan da Muka Koya a Azumin Bana
- Hamas ta kashe sojojin Isra’ila bayan harba rokoki 1,500
“Duk mai bayani kan inda mutanen suke dangane da kudaden samar da gidaje ga ma’aikata da suka handame, yana kai rahoto ga Hedikwatar ICPC da ke Abuja ko ofisoshinta a jihohi ko ofishin ’yan sanda mafi kusa,” inji sanarwar.
Kumo, tsohon Daraktan Gudanarwa ne, na bankin ‘Federal Mortgage’ ne lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.
ICPC na neman mijin na ’yar Shugaba Buhari, Fatima, tare da Tarry Rufus da kuma Bola Ogunsola ruwa a jallo.
Sai dai har yanzu Fadar Shugaban Kasa ba ta ce uffan ba dangane da neman da ICPC ke yi surukin na Shugaban Kasa da sauran mutanen.