Faisal, dan tsohon Shugaban Kwamitin Gyaran Fansho na Kasa, Abdulrasheed Maina, wanda ke fuskantar shari’a bisa zargin badakalar kudade ya tsere zuwa kasar Amurka.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da ke gurfanar da Faisal ce ta sanar da haka a lokacin zaman kotun da Mai Shari’a Okon Abang ke jagoranta a Abuja.
- Maganin gargajiya ya kashe yara ya kwantar da mahaifiyarsu a Kano
- Matakan soyayya da bayaninsu dalla-dalla
- ’Yar aiki ta rataye kanta a Kano
- Gwamnatin Kano ta rufe masallacin Sheikh Abduljabbar kan ‘batanci ga Sahabbai’
Lauyan EFCC, Mohammed Abubakar ya shaida wa kotun cewa Hukuamr ta samu bayani cewa wanda ake zargin ya sulale zuwa Jamhuriyar Nijar daga nan kuma ya arce zuwa Amurka.
A zaman kotun na ranar Alhamis, Mai Shari’a Okon Abang, ya umarnci wanda ya tsaya wa Faisal, Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Kaura-Namoda ta Jihar Zamfara, Hon. Sani Dan-Galadima, ya sarayar da kadararsa da ya jingiyar wa kotun da yake wakiltar matashin.
An ba da belin wanda ake zargin ne a kan Naira miliyan N60 bisa sharadin dole wanda zai tsaya masa ya kasance dan Majalisar Tarayya.
A watannin baya EFCC ta tiso kayar mahaifin Faisal, Abdulrasheed Maina wanda ke fusknatar zargin ta’ammali da haramtattun kudade, daga Jamhuriyar Nijar, inda ya tsere bayan kotu ta ba da belin shi.
Tuni dai lauyan Abdulrasheed Maina, Adeola Adedip da Sanata Muhammad Ali Ndume wanda ya tsaya aka ba da beliln shi suka janye hannunsu a kansa.
Tun daga nan kuma kotu ba ta sake ba da belin Abdulrasheed Maina ba.