✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP

Jam'iyyar ta ce gazawar da APC ta yi ne, ya sa da wuya a samu wanda zai yi tallan ta a 2027

Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa babu wani ɗan Arewa mai mai hankali da zai goyi bayan APC a zaɓen 2027.

PDP ta bayyana hakan ne a matsayin martani kan zargin cewa Sanata Lawal Adamu, Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, baya aikin komai sai ɗumama kujera.

Haka kuma, ana zargin gwamnatin Jihar Kaduna da dakatar da rarraba kayayyakin koyarwa da Sanata Lawal Adamu ya saya domin amfanin makarantun jihar.

Yusuf Dingyadi, Mataimaki na Musamman na Shugaban PDP kan Yaɗa Labarai, ya ce ya kamata gwamnatin jihar ta haɗa kai da wakilan jama’a don ci gaban al’umma.

“Abin da ake buƙata shi ne gwamnatin jihar, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, ta haɗa kai da sauran wakilan jama’a don inganta rayuwar al’ummar Kaduna.

“PDP jam’iyya ce mai aƙida, kuma idan har kuna ci gaba da kai mata hari, ba za ku taɓa samun ci gaba ba.

“Ba za ku iya ɗaukar ’yan daba da masu yaɗa farfaganda don ɓata mana suna ba, kawai don ku burge Shugaba Bola Tinubu saboda burinku na 2027.

“Babu wani ɗan Arewa mai hankali da zai yi wa APC kamfe a Arewa.

“Gaskiyar ita ce, wasu ’yan siyasa suna yi masa biyayya ne ba don suna goyon bayansa da gaske ba, sai dai kawai don su samu abinci,” in ji shi.

Dingyadi ya shawarci Gwamna Uba Sani da kada ya bari wasu ’yan siyasa su ruɗe shi.

Ya ƙara da cewa, “’Yan majalisar da PDP ta zaɓa suna aiki tuƙuru. Suna yin ƙoƙari a yankunansu sama da na APC.

“Ba za ku iya daƙile nasarar siyasarmu ta hanyar ɗaukar ’yan farfaganda don su kai wa wakilanmu masu aiki hari ba, ko kuma ta hanyar shirya ficewar ’yan siyasa daga PDP a wuraren da aka shirya da gangan.”