✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Babu wata maboyar ’yan bindiga da aka gano a kusa da hedikwatar ’yan sanda a Abuja’

An yada rade-radin cewa an gano wata maboyar ’yan bindiga a kusa da hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja.

Hukumar ’Yan Sanda ta musanta rade-radin da ke yawo cewa an gano maboyar ’yan bindiga a kusa da hedikwatarta da ke Abuja.

Kakakin ’yan sandan Abuja, Olumuyiwa Adejobi, ya sanar ta shafinsa na Twitter cewa bidiyon karya ne ake yadawa, inda ya shawarci mazauna yankin birnin tarayya da kada su firgita.

Sakon nasa ya ce, “Labarin karya: Ba a gano wani wurin garkuwa da mutane ba a kusa da hedikwatar ’yan sanda, a Garki Abuja.

“Labaran ko bidiyon da ake yadawa kuskure ne kawai kuma makircin makiya don ci gaba da haifar da fargaba a tsakanin mazauna Abuja da ’yan Najeriya gaba daya.”

Ya kara da cewa, har yanzu ’yan sanda na ci gaba da kai hare-hare da kuma lalata gidaje da ka iya zama maboyar masu aikata laifuka a Abuja.

“Duk da haka bari na sake nanata cewa rundunar ’yan sanda ta babban birnin tarayya Abuja bisa umarnin Babban Sufeto, ta fara kai samame don lalata wasu gidaje da ka iya zama maboya ga masu aikata laifuka a Abuja.

“Don haka babu wani abun fargaba saboda mun dauki matakan da suka dace don dakile ayyukan ’yan ta’adda da masu aikata laifuka a cikin Abuja da kuma fadin Najeriya.”