Babban Bankin Najeriya (CBN), ya takaita yawan kudin da mutum zai iya cirewa na’urar POS a rana daya zuwa N20,000, a banki kuma ba za su wuce N100,000 ba a mako guda.
Hakan da daya daga cikin irin matakan da babban bankin ya ce zai fito da su domin takaita yawon tsabar kudi a hannun mutane.
- Dan sanda ya mutu a musayar wuta da ’yan bindiga a Ebonyi
- NAJERIYA A YAU: Yadda Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Ya Dawo Aiki
Ana sa ran wannan tsari ya soma aiki ya zuwa ranar tara ga watan Janairu, 2023.
Wannan na zuwa ne a lokacin da CBN ke shirye-shirye sakin sabbin takardun Naira da aka sake wa fasali don fara kashewa daga ranar 15 ga Disamba.
Wannan bayanin na kunshe ne a cikin sanarwar da CBN ya fitar ranar Talata mai dauke da sa hannun Darakta a bankin, Haruna Mustafa.