✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu wanda ya hana Tinubu zuwa Amurka – Festus Keyamo

Ya ce 'yan adawa ne ke yada cewa Amurka na neman Tinubu ruwa a jallo

Kakakin Kwamitin Yakin Neman Zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, Festus Keyamo ya gabatar da shaidar bizar da Amurka ta ba dan takararsu ta shiga kasarsu, sabanin yadda ya ce wasu na cewa kasar na nemansa ruwa a jallo.

Kakakin ya saka wani hoton bizar da Amurkan ta ba Tinubu na shigar kasar a shafinsa na Twitter ne a daren Asabar.

“Ga ‘yan adawa da sauran ‘yan gaza-gani da ke yada jita-jita da karairayi na Amurka ta hana Bola Ahmed Tinubu izinin shiga kasar, toh, ga shaidar cewa ba haka ba ne, gani dai ya kori ji,” inji Keyamo.

Masu rade-radin dai na cewa sakamakon hana shi bizar ta sa Tinubu ya daga tafiyarsa zuwa Amurka.

A makon da ya gabata Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu ta fitar da wata sanarwa inda ya ce dan takarar zai je ziyara zuwa wasu kasashen waje daga ranar hudu ga watan Disamban 2022.

Kwamitin ya kuma ce Tinubu zai kai ziyara kasashen ne don ganawa da shugabanninsu, kan takarar da yake yi na zama Shugaban Najeriya.

Sanarwar ta ce Tinubu zai kuma ziyaraci birnin Landan a inda zai yi jawabi a Chatham House ga manyan masu fada a ji, da kuma gudanar da tsare-tsare na kasar Birtaniya.

Shi ma Sanata Orji Kalu a wani sako a shafin sa Facebook ya ce Ma’aikatar Harkokin Waje ta Amurka ta tabbatar masa da cewa za ta karbi bakuncin Tinubu a makon karshe na watan Disamba.