✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu ba mu kammala tabbatar da El-Rufai a matsayin minista ba — Majalisar Dattawa 

Majalisar ta ce tana jiran rahoton jami'an tsaro a kan El-Rufai da wasu kafin tabbatar da su a matsayin ministoci.

Majalisar Dattawa ta ce har yanzu ba ta kammala tabbatar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu mutum uku a matsayin minista.

Sauran mutum biyu da majalisar ta ce ba ta tabbatar ba, sun hada da Sani Abubakar Danladi daga Jihar Taraba da Stella Okotete daga Jihar Delta.

Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya ce suna jiran rahoton jami’an tsaro kafin su tabbatar da mutanen uku.

Kawo yanzu dai su kadai ne ba su shiga cikin mutum 48 ba da majalisar ta tabbatar a ranar Litinin, amma ta tantance su a makon da ya wuce.

Kazalika, an shiga rudani a majalisar yayin tantance Festus Keyamo a matsayin daya daga cikin wadanda Shugaba Bola Tinubu zai bai wa mukamin minista.

Daga baya Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya isa Fadar Shugaban Kasa bayan zazzafar muhawarar da ta barke a zauren majalisar yayin tantance babban lauyan daga Jihar Delta.

Gabanin haka dai, majalisar ta soma shiga zaman sirri saboda sabanin da ya rincabe tsakanin sanatoci a kan tantance Mista Keyamo.

Sanata Darlington Nwokocha ne, ya fara gabatar da kudirin dakatar da tantance Keyamo a gaban majalisa, inda ya nemi a dakatar da shi har sai lokacin da ya amince da cewa majalisa na da damar bincikar ayyukan ministoci.

Hakan ya faru ne sakamakon tirjiyar da ya nuna a lokacin da yake minista a baya, inda ya ki amsa gayyatar majalisa.

Kudirin ya samu goyon bayan mafi rinjayen sanatoci, hakan ya sa daga karshe majalisar ta yanke shawarar shiga zaman sirri kan lamarin.

Festus Keyamo dai, shi ne ministan gwamnatin Buhari da ya sake shiga cikin jerin sunayen wadanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai nada a matsayin minista.