✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu wanda aka kashe a zanga-zangar yunwa a Kano —’Yan sanda

An kama mutane 873 kan lalatawa da sace dukiyoyin jama'a da na gwamnati a lokacin zanga-zangar a Kano

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Salman-Dogo Garba, ya ce rundunar ba ta da labarin asarar rai a lokacin zanga-zangar yunwa da tsadar rayuwa da aka gudanar.

Kwamishinan ya bayyana haka ne ranar Litinin a lokacin ganawarsa da ’yan jarida, inda ya ce rundunar ta kama mutane 873 kan laifin lalatawa da sace dukiyoyin jama’a da na gwamnati a lokacin zanga-zangar.

“A iya bayanan da muke da su, zuwa yansu ba mu da rahoton asarar rai a yayin zanga-zangar,” in ji shi.

Sai dai Aminiya ta kawo rahoton iyalan wasu matasa akalla uku da aka kashe a lokacin zanga-zangar, ciki har da wata budurwa da ake shirin daura aurenta.

Iyalan sun kuma yi zargin sun rasu ne a sakamkon harbi daga jami’an tsaro, musamman ’yan sanda.

Iyalan wadanda suka rasun dai sun bayyana damuwa bisa yadda zanga-zangar da aka shirya ta lumana ta yi ajalinsu, inda suka bukaci a bi musu hakkinsu.

Zanga-zangar lumanar ta rikide zuwa tarzoma ne bayan da bata-gari suka kwace ta, suka rika fasa wurare suna sace-sace, tare da jikkata mutane a sassan jihar.

An yi dauki ba dadi tsakanin bata-garin da jami’an tsaro a kofar gidan gwamnatin jihar da sauran sassan jihar, inda aka kama sama da mutum 100.

Kazancewar lamarin ya kai ga gwamnatinn jihar, Abba Kabir, sanya dokar hana fita tsawon awa 24, kafin daga bisani a sassauta dokar.