Hukumar Yi wa Kasa Hidima a Najeriya NYSC, ta ce ba ta da wani shiri na bai wa masu yi wa kasar hidima horon tafiya yaki.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Sadarwa na hukumar, Emeka Mgbemena ya fitar a ranar Juma’a.
- Duk wani shirin na durkusar da Gwamnatin Buhari zai gaza — APC
- Dubun manomin da ya zuba guba a rijiyoyi 9 ta cika
A cewarsa, Darakta-Janar na hukumar ya bayyana cewa bisa Tsarin Harkar Tsaron Kasa, masu yi wa kasa hidimar sun kasance tamkar sojojin ko ta kwana saboda iliminsu da gogewarsu wanda hakan ya sa cikin sauki za su iya karbar horon sojin.
A dalilin haka ne ya bukaci masu yi wa kasar hidima su zama masu kishin kasa domin dorewar shirin na NYSC a Najeriya.
Jami’in ya ce babu lokacin da Shugaban na NYSC ya taba bayyana cewa za a tura masu yi wa kasar hidima fagen daga domin yaki da masu tayar da kayar baya.
Ya ce sabanin rahotannin da wasu jaridun kasar suka wallafa, shirin na NYSC zai ci gaba da kare muradun masu yi wa kasa hidimar a kowane lokaci.