✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu sabani a tsakanin Ronaldo da Platini -Mai magana da yawun UEFA

Mai magana da yawun Hukumar shirya kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) Pedro Pinto ya ce rade-radin da wasu ke bazawa na cewa akwai sabani…

Mai magana da yawun Hukumar shirya kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) Pedro Pinto ya ce rade-radin da wasu ke bazawa na cewa akwai sabani a tsakanin dan kwallon Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo da kuma shugaban Hukumar UEFA Mista Michel Platini sam ba gaskiya ba ne.
Kulob din Madrid dai bai ji dadin zancen da Platini ya yi ba a watan Oktoban da ya wuce inda ya nuna bai dace Ronaldo ko Messi su lashe Gwarzon dan kwallon duniya a wannan karo ba sai dai Golan Jamus Manuel Nueur ganin yadda golan ne ya taimaki Jamus ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da ya gudana a Brazil a watan Yulin bana.
Shugaban ya ce yakamata a ce duk dan kwallon da ya fi nuna kwazo a gasar cin kofin duniya ne ya kamata ya rika lashe kyautar a shekarar da gasar ta gudana, tun da kofin duniya ya fi kowane kofi karfi da daukaka a duniya.
A gasar cin kofin duniya da aka yi a bana, Ronaldo bai yi rawar gani ba hasalima an fitar da kasarsa Fotugal tun a zagayen farko, yayin da Messi kuma ya kai Ajantina wasan karshe amma bai samu nasarar  lashe kofin ba sannan kuma ba shi ne dan kwallon da ya fi zura kwallo a raga a gasar ba amma golan Jamus Manuel shi ya taimaki Jamus ta lashe kofin da hakan ta sa Jamus ta sake lashe kofin a karon farko tun bayan shekara 24.
A ranar Asabar da ta gabata bayan da kulob din Real Madrid ya lashe gasar cin kofin Club World Cup a wajen rabawa ’yan kwallon kyaututtuka kuma sun yi layi suna yin musabaha da jami’an Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da kuma na UEFA ciki har da Michel Patini amma Ronaldo ya tsallake Platini ba tare da sun yi musabaha ba, al’amarin da ya sa wasu suka rika zargin yana fushi da shugaban ne akan kalaman da ya yi a kansa a watan Oktoba.
Hakan ce ta sa mai magana da yawun Hukumar UEFA Mista Pedro Pinto ya fito ya bayyana wa duniya cewa babu wani sabani a tsakanin mutanen biyu, hasalima tuni shugaban ya ba da hakuri a kan kalaman da ya yi.  Ya ce Platini yana mamakin yadda ake baza jita-jitar ba ya shiri da Ronaldo.  “A iya sanina Ronaldo yana daga cikin ’yan kwallon da nake alfahari da su a fadin duniya”, inji shi a wata sanarwar da ya fitar a kwanakin baya.
Ya ce tun kafin a yi wasan karshen, Ronaldo da Platini suka yi musabaha, don haka idan dan kwallon bai sake gaisawa da shi a lokacin da ake raba musu kyaututtuka a karshen wasan ba, babu wani aibu.  Hasalima a lokacin da Ronaldo yake kokarin gaisawa da Platini a daidai lokacin ne Kocin Madrid Carlo Ancellotti yake tattaunawa da shi al’amarin da ya sa Ronaldon ya wuce ba tare da sun gaisa ba.