Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC) Ibrahim Magu ba ya hannunta.
A amsar wasikar neman belin Magu da lauyansa Tosin Ojaomo ya aika wa rundunar, Sufeta Janar na ‘Yan Sanda Mohammed Adamu ya ce Magu ba ya tsare a hannun runudnar kuma ba a hannunta belinsa yake ba.
Wasikar Babban Hadimin Shugaban ’Yan Sandan DCP Idowu Owohunwa ta ce, “Sufeta Janar na ’Yan Sanda na shawartar ka da ka gabatar da bukatar taka ga shugaban kwamitin binciken domin yin abin da ya dace”.
Tun ranar Litinin din makon jiya da jami’an tsaro na DSS suka tisa keyar Magu zuwa gaban kwamitin na tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara, Mai Sharia Ayo Salami da ke binciken zarginsa da aikata wasu laifuka yake tsare.
Lauyan Magu ya koka bisa rashin bayar da belinsa da kuma kin ba shi sarari ya samu ya kare kansa daga zargin da ake masa, yana mai kira ga rundunar ‘yan sanda da ta bayar da belin sa.
Amma amsar da rundunar ta aika wa lauyan na Magu ta ce Sufta Janar “na so ka fahimci cewa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ba ta bincikar CP Ibrahim Magu kuma ba ita ke tsare da shi ba, kwamitin da Shugaban Kasa ya kafa na bincikar ayyukan EFCC ne ke tsare da shi”, inji shi
Magu na tsare a hannun jami’an tsaro yayin da kwamitin na Mai Shari’a Ayo Salami ke ci gaba da bincikar ayyukan EFCC karkashin jagorancinsa.
Binciken ya yi sanadiyyar dakatar da shi da daukacin manyan darektoci da wasu manyan jami’an humukar cikin mako guda tare da nada Mohammed Umar a matsayin mukaddashin shugaban hukumar.
Ministan Shari’a Abubakar malami ya ce an dauki matakin dakatarwar ne domin ba wa kwamitin damar yin cikakken bincike a hukumar.
Binciken ya samo asali ne daga korafin da Malami y aiki wa Shugaban Kasa na zargin magu da wasu laifuka 12 masu alaka da karkatar da dukiyar gwamnatin da aka kwato da rashin biyayya ga ministan da sakaci da aiki da kuma nuna bambanci a tsakanin jami’an hukumar.