✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu rikicin shugabanci a Miyetti Allah- Bello Bodejo

Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore Alhaji Bello Abdullahi Badejo ya ce babu wani rikicin shugabanci da ya dabaibaye kungiyarsu har ta kai ga dakatar da…

Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore Alhaji Bello Abdullahi Badejo ya ce babu wani rikicin shugabanci da ya dabaibaye kungiyarsu har ta kai ga dakatar da shi.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jarida a Abuja shekaranjiya Laraba.
Ya ce har yanzu shi ne shugaban kungiyar kuma wadanda suka fitar da sanarwar dakatar da shi ba ’yan kungiyarsu ba ne.
Ya ce “maganar dakatar da ni ba ta da tushe ballantana asali, domin shugabannin wannan kungiya na kasa babu wanda yake da masaniyar hakan. Kuma ya zo daidai lokacin da muke aiki zagaya jihohi domin wayar da kan mutane, musamman wadanda ba Fulani ba, kan yadda za su zauna da Fulanin, domin a samu zaman lafiya mai dorewa.
Dangane da wadanda suka fitar da sanarwar dakatar da shi sai ya ce, “To, ka san a kasar nan muna kungiyoyin Fulani da yawa, daga cikin sanannu akwai Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, wadda ta fada rikici da yawa kafin daga bisani ta kamo bakin zare, sakamakon tsakani da Sarki Musulmi Sultan Abubakar na II ya shiga. To wadanda suka taka rawa wajen haifar da matsala a waccan kungiya, bincikenmu da muka gudanar bayan ganin labarin a jarida ya nuna mana su ne suka fado nan domin bata mana tsari, duk da cewa ba membobin kungiyarmu ba ne.
Ya ce kungiyarsu ta saya wa Shugaba Jonathan fom don kare mutuncin Fulani.
“Idan muka kalli Najeriya za mu ga ko’ina akwai Fulani, amma a haka kananan kabilu ke yi mana cin kashi. Mun zauna tare da membobin kungiyarmu gaba daya mun tattauna. Mun lura da cewa rayukan Fulani da yawa a yankin Kudancin Kaduna na salwanta a lokutan zabe, kuma ba tare da an dauki wani kwakkwaran mataki ba. Haka zalika Kudancin kasar shi ma an kashe Fulani ba tare da dalili ba. Saboda a matsayina na shugaban hakkina in nemi shawarar shugabannin kan ta wace hanya za mu kawar da kowace irin fitina wadda muka san za ta shafi Fulani.
“Daga cikin shawarwarin da muka gabatar mun kallin cewa gwamnati mai ci ita ke da ’yan sanda da sojoji da sauran jami’an tsaro. Idan yau batun kare Fulani ya zo kafin mutumin da yake Abuja ya farga, wadannan jami’an tsaro ne za su kai musu dauki. Yanzu zabe ya karato da bai wuce wata hudu ba, saboda haka ba zan zuba ido abin da ya faru da Fulani a zaben 2011 ya sake faruwa a kansu ba. Saboda haka, kasancewar gwamnati na da sojoji da ’yan sanda, ba mu da hurumin yin fada da ita, balle mu ce gaba daya babu ruwanmu da ita. Wannan dalili ya sa muka ce dole mu yi tafiya da gwamnati mai ci.” Inji shi.
“A sanarwar da muka fitar a baya, mun ce muna tafiya tare da gwamnati mai ci, a Najeriya kuma ba Jonathan ne kawai shugaba mai ci ba. Idan kuma mu kalli ita kanta gwamnatin za mu ga akwai Fulani masu yawan gaske wadanda ke rike da mukamai. Misali irin su, Adamu Mu’azu, Sanata Bala Muhammad, Farfesa Rufa’i Alkali da sauransu, babu yadda za a yi mu watsa mu kasa a ido, musamman yadda aka san Fulani da biyayya ga magabata. Kuma manyanmu ne na kungiya gaba daya muka hadu muka saya wa Jonathan Fom domin marasa baya don guje wa abin da ya faru da mu a lokutan baya. Wannan ya kara nuna cewa kanmu hade yake, tun da har za mu iya haduwa wajen goyon bayan gwamnatin da za ta ba mu ‘yan sanda da sojoji wajen kare rayukan Fulani da dukiyoyinsu. Saboda ba Jonathan muka saya wa fom ba, kanmu muka saya wa.
A karshe ya bukaci Fulani su mallaki katin zabe domin shi ne babban makaminsu, kasancewar idan ba sa za su yi zabe ba, babu gwamnatin da za su kai mata kukansu ta saurare su, saboda ba za su amfane ta da komai.