✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu mulki mafi muni a tarihin Nijeriya kamar na Buhari — SDP

Gwamnatin Tinubu ta yi gaggawa wajen kawo wasu sauye-sauyen masu tsauri ga tattalin arziki a ƙasar.

Shugaban jam’iyyar SDP na Najeriya, Shehu Gabam ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da ta gabata da rashin magance matsalolin Najeriya, lamarin da ya ce ya haifar wa gwamnati mai ci tarin matsalolin tattalin arziki.

Yayin wata hira a shirin ‘Politics Today’ na gidan Talbijin na Channels a ranar Juma’a, Gabam ya zargi gwamnatin Buhari da gazawa wajen magance matsalolin ƙasar.

”Na sha faɗa a lokuta da dama cewa gwamnatin Buhari ita ce gwamnati mafi munin gwamnati da aka taɓa gani na tarihin Najeriya.

“Mulkinsa [Buhari] ne ya gadar wa gwamnatin Bola Tinubu matsin tattalin arzikin da take fuskanta a yanzu,” in ji Gabam.

Shugaban na SDP ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta yi gaggawa wajen kawo wasu sauye-sauyen masu tsauri ga tattalin arziki a ƙasar.

“Mun sani ya gaji matsalar tattalin arziki, haƙƙinsa ne ya lalubo hanyoyin farfaɗo da shi, amma bai kamata hanyoyi su zama masu tsauri ba, saboda ba za ka iya farfaɗo da shi a rana guda ba,” in ji Gabam.

Tun bayan hawansa mulki, shugaba Tinubu ya ɗauki matakai da dama wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar, ciki har da cire tallafin man fetur da ya yi a jawabinsa na farko bayan shan rantsuwa, lamarin da masana ke alaƙantawa da ƙara jefa ƙasar cikin matsin rayuwa da ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki.

Ko a watan Afrilu ma hukumar ƙididdiga ta ƙasar NBS ta ce hauhawar farashi ya kai kashi 33.69.