Babban Mai Tsawatarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya ce matar dan takarar Shugaban Kasa a APC, Oluremi Tinubu za ta raba gardamar takaddamar da ake yi kan daukar Musulmi a matsayin Mataimaki kasancewarta Fasto.
Siyasar dai ta yi zafi ne kan yiwuwar samun tikitin tsayawa takarar Musulmi da Musulmi a jam’iyyar APC mai mulki.
- Majalisar Dokokin Kano ta bai wa Ganduje damar karbo bashin N10bn
- ‘Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ne ya hana ta ci gaba’
Sai dai Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta gargadi manyan jam’iyyun kasar nan kan bai wa mabiya addini daya tikitin takarar.
Amma wasu masu ruwa da tsaki sun bukaci ‘yan Najeriya da su mai da hankali kan cancanta fiye da bambamcin addini.
Da ya ke jawabi ga manema labarai a zauren majalisar a ranar Laraba, Orji Kalu, ya bukaci Kiristoci da kada su ji tsoro tun da matar Tinubun Fasto ce.
“Bari na fada muku, a gidana, matata ce shugabar gidan a zahiri. Ko ku mazan da suke nan, yanzu da matanku ba sa nan, su ne shugabannin gidan. Matarka ce za ta baka damar saka kayan da suka dace da kai.
“Matarka za ta ce maka ga abin da ya kamata ka ci; koko ko kosai. Ko ka yi gardama daga karshe zabinta za ka bi, kuma idan ta ce a biya kudin makarantar yara haka za ka biya babu jayayya.
“Ya kamata Kiristoci su kwantar da hankalinsu domin matar Tinubu fasto ce, za mu samu kariya. Tana da ilimin siyasa,” inji shi.
Matar Tinubu, wacce a halin yanzu ke wakiltar Legas ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, an nada ta a matsayin Mataimakiyar Fasto ta cocin RCCG a 2018.
Dan takarar Shugaban Kasar na APC na daga cikin wadanda suka halarci bikin nadin nata.