Shugaban bangare na jam’iyyar APC a matakin kasa Victor Giadom ya ce jam’iyyar ba ta da mafita daga rikicin shugabancin da take ciki face kiran taron Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC).
Giadom wanda ya yi magana jim kadan bayan jam’iyyar reshen jiharsa ta Ribas ta dakatar da shi daga jam’iyyar a ranar Litinin ya kwatanta matakin a matsayin abin dariya, yana mai cewa dole a kawo karshen gaba-gadin da wasu ke yi a jam’iyyar.
“Na sha fada tun da farko cewa mafita daya daga wannan rikicin ita ce a damka harkokin jam’iyyar a hannun wandan suka fi iko kuma dole sai an kira NEC domin a kawo karshen wannan shirmen a kuma a samu kwanciyar hankali.
“Dole a yi NEC domin shi ne gaba da Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) kuma gaba da kowa, amma ban san me suke jin tsoro ba.
- APC ta dakatar da Giadom a Ribas
- Kotu ta tsawaita wa’adin Giadom a matsayin shugaban APC
- Zaben Edo: Ize-Iyamu ya lashe zaben fid da gwanin APC
“A mika jam’iyya ga wadanda suka fi karfin iko domin a yi abin da ya fi dacewa sannan a yanke hukunci a kan duk wani mataki da shugabannin jam’iyya suka dauka. Don haka idan ba a yi taron NEC ba da wuya a magance wannan rikicin”, inji shi.
Da yake magana game da matakain jam’iyyar na maye gurbinsa da Worgu Boms a matsayin Mataimakin Sakatare na Kasa, Giadom ya ce, “Babu yadda za a yi mutum ya zama dan NWC ba tare da an yi zabe kuma shi wanda ake maganan ya yi takara ya ci zabe ba”.
A baya dai Giadom ya rubuta wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) takarda a ranar 18 ga watan Yuni, a matsayinsa shugaban bangare na jam’iyyar APC na riko, cewa kada INEC ta amince da zaben dan takarar gwamnan jam’iyyar na jihar Edo domin ba da yawunsa za a yi ba.