Kungiyar Yarabawa ’yan jam’iyyar APC mazauna unguwar Sabon Gari da ke Kano ta ce sam babu hannun Shugaban Kasa Bola Tinubu a soke zaben Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, da kotun daukaka kara ta yi.
Shugaban kungiyar, Seyi Olurunsola, ne ya bayyana hakan yayin wata zantawarsa da manema labarai a Kano ranar Juma’a.
Ya ce ɓangaren shari’a cin gashin kansa yake yi kuma yana da damar yanke hukunci a kan dukkan shari’un zaben 2023 da sauran dukkan kararraki.
Wata kungiya mai rajin kare muradun Yarabawa mai suna CYCK ce dai ta yi zargin Fadar Shugaban Kasa na tsoma baki a kan shari’un kotun ɗaukaka ƙarar.
Amma a cewar Seyi, sam babu ruwan Shugaban Ƙasa a yin katsa landan kan harkar saboda mutum ne daya yi amanna da ba kowanne bangare na gwamnati damar cin gashin kansa.
Ya kuma ce Yarabawa sun shahara da zaman lafiya da mutanen duk yankin da suka tsinci kansu a ciki, kamar yadda suka nuna a zaɓen da ya wuce ta hanyar zabar APC tun daga ƙasa har sama.
“Kowa ya san lamarin zabe a yi nasara ne ko kuma a faɗi, kuma a bayyane yake cewa NNPP ta faɗi zaben Gwamnan Kano da ya gabata, kamar yadda hukunce-hukuncen kotuna biyu ya nuna, don haka kamata ya yi kawai su rungumi ƙaddara,” in ji Shugaban kungiyar Yarabawan.