Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Obadiah Mailafiya ya ce gwamanti ba ta da hannu a kashe-kashen da ake yi kuma ba shi da hujjar cewa ana wa rayuwarsa barazana.
Mailafia ya bayyana haka ne bayan fitowarsa daga ofishin hukumar tsaro ta DSS a Jihar Filato, wanda shi ne karo na uku na zuwansa ofishin hukumar domin amsa tambayoyi.
- Karin farashi: TUC ta aike wa gwamnati takardar gargadi
- An kama su suna yin fim din batsa a wurin ibada
“Ba ina nufin cewa gwamnati na da hannu a kashe-kashen ba ne. Ina nufin za ta iya yin fiye da abin da take yi saboda ana kashe dubban mutane.
“Na riga ya na bayyana cewa ba ni da hujjar cewa rayuwata na cikin hadari, kawai dai na na samu barazana ne a inda nake zaune.
“Ranar Alhamis ce na ga wasu bakin fuska na kokarin yin kutsawa a inda nake saboda haka sai na tsallake katanga saboda ni ban san su ba.
“Yanzu na su ofishin DSS na Filato ne kamar yadda na saba. Na yi farin cikin yadda aka tarbe ni cikin kwarewa, babu wata barazana ko tsoratarwa”, inji shi.
Karo na uku ke nan yana Mailafia ke bayyana a ofishin DSS, tun wani zargi da ya yi a baya cewa wani gwamna mai ci ne kwamandan kungiyar Boko Haram wanda ya ce sun hada baki da ‘yan bindiga domin tayar da zaune tsaye a Najeriya.
Daga baya ya yi watsi da zargin ya yi, wanda ya ce wasu ne da ya hadu da su a kasuwar kauye suka gaya masa abin da ya fada.