Rundunar ‘yan sandan Kano ta ce mutumin da aka yayata cewar an tsinci gawarsa a kan titin zuwa Gidan Gwamnatin Kano na nan da ransa.
Kakakin Rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan, yana mai cewa mutumin da hannunsa ya ɗaura wa kansa igiyar da aka gani a wuyansa ake kuma zargin da ita aka kashe shi.
- Majalisa ta dakatar da Sanatan da ya ce an yi cushen N3trn a Kasafin Kuɗi
- ’Yan bindigar da suka sace ɗaliban Tsangaya a Sakkwato sun buƙaci fansar N20m
Idan za a iya tunawa dai, a jiya ne aka wayi gari da ganin mutumin yashe a kan titin zuwa Gidan Gwamnatin Kano da igiya ta shaƙe wuyansa, dalilin da aka yi zargin ɓata-gari ne suka halaka shi.
Sai dai a safiyar ranar Talata ne kakakin rundunar ’yan sandan Kano ya musanta hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce yanzu haka mutumin na hannunsu har zuwa lokacin da za su kammala bincike.
“Bayan mun kai shi asibiti ya faɗi gaskiya. Ba abin da aka kwata a wajensa. Hasalima shi ya sawa kansa kebir ya kwanta a wajen. Yanzu haka yana hannun ’yan sanda,” in ji Kiyawa.