9. An karbo daga Isma’il dan Abu Uwais ya ce: “Malik ya ba ni labari daga Abdullahi dan Dinar bawan Abdullahi dan Umar daga Abdullahi dan Umar dan Khaddab (RA), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Hakika misalinku da Yahudu da Nasara (Kiristoci) kamar wani mutum ne da ya yi jinga da wasu ma’aikata. Ya ce, “Wa zai yi mini aiki zuwa rabin yini bisa kiradi daidai? Sai Yahudu suka yi aiki zuwa rabin yini bisa jingar (lada) kiradi daidai. Sa’an nan Nasara (Kiristoci) suka yi aiki bisa jingar kiradi daidai, sa’an nan ku ne wadanda za ku yi aiki daga Sallar La’asar zuwa buyar rana bisa jingar kiradi bibbiyu. Sai Yahudu da Nasara su yi fushi su ce: “Mu muka fi yawan aiki amma muka fi karancin lada (sakamako).” (Allah) Ya ce, “Shin na zalunce ku wani abu daga hakkinku? Suka ce, “A’a.” Ya ce, “Wannan ita ce fifitawaTa (falala) ina bayarwa da ita ga wanda Na so.”
Babi na Goma: Laifin wanda ya hana (ki biyan) hakkin dan kwadago:
10. An karbo daga Yusuf dan Muhammad ya ce: “Yahya dan Sulaim ya ba ni labari daga Isma’il dan Umayya daga Sa’id dan Abu Sa’id daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce, “Allah Madaukaki Ya ce: “Mutum uku Ni ne mai yin husuma da su, (abokan gabaNa) Ranar kiyama: (1) Mutumin da aka hada shi da Ni ya yi yaudara. (2) Da mutumin da ya sayar da dan Adam mai ’yanci ya ci kudinsa. (3) Da mutumin da ya yi jinga da wani mutum, ya gama masa aiki bai biya shi ladarsa ba.”
Babi na Goma Sha daya: Wanda ya yi jinga da wasu daga La’asar zuwa dare:
11. An karbo daga Muhammad dan Ala’u ya ce: “Abu Usamata ya ba mu labari daga Burdata daga Abu Burdata daga Abu Musa (Allah Ya yarda da shi) daga Annnabi (SAW) ya ce: “Misalin Musulmi da Yahudu da Nasara (Kiristoci) kamar misalin wani mutum ne da ya yi jinga da wasu mutane wadanda za su yi masa aikin farko yini zuwa dare bisa wani lada (sakamako) sananne. Wasu suka yi aiki har zuwa rabin yini, sai suka ce, “Ba mu da wata bukatar ladarka game da aikin da ka shardanta mana, abin da muka aikata ya zamo batacce (babu biya). Sai ya ce, musu a’a kada ku aikata haka, ku ci sauran aikinku domin ku karbi ladarku cikakke. Sai suka ki cikawa suka bari. Sai ya yi jinga da wasu ma’aikata a bayansu, ya ce: “To ku, ku cika sauran yininku wannan kuna da ladar abin da na shardanta gare su na (jama’ar) farko. Sai su yi aiki har zuwa lokacin Sallar La’asar, sai su ce, “Abin da muka aikata maka mun bar ladarsa bisa ga abin da ka shardanta muna cikinsa (ba za mu iya gamawa ba). Sai ya ce, musu: “Ku cika aikinku kuna da sauran abin da ya rage daga yini saura kadan ne, sai su ki sai ya yi jinga da wasu jama’a da su yi masa aikin sauran yini har rana ta buya, su cika sauran aikin bangaren nan biyu da suka gabata. Wannan shi ne misalinsu (Musulmi) da misalin abin da suka karba daga wannan hasken (Alkur’ani).” Da wannan kasdalani ya ce, “Allah Ya bata aikin Yahudu don ba su yi imani da Isa (AS) ba, haka Nasara (Kiristoci) aikinsu ya baci don sun ki imani da manzancin Annabi Muhammad (SAW).