554. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Humaid daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Abu dayyib ya yi wa Manzon Allah (SAW) kaho, sai ya umurta da a bashi sa’i daya na dabino. Kuma ya umurci shugabansa da ya saukaka masa daga harajinsa (saboda Abu dayyib bawa ne).”
555. An karbo daga Musaddad ya ce: “Khalid dan Abdullahi ya ba mu labari, ya ce, Khalid ya ba mu labari daga Ikramata daga dan Abbas (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya yi kaho, kuma ya yi kyauta ga mai yin kaho da haramun ne da bai ba shi komai ba.”
Babi na Arba’in da daya: Kasuwancin abin da aka hana daurawa ga maza da mata:
556. An karbo daga Adamu ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari ya ce, Abubakar dan Hafsu ya ba mu labari daga Salim dan Abdullahi dan Umar daga Babansa ya ce: “Annabi (SAW) ya aika wa Umar (Allah Ya yarda da shi) da wani tufafi na hariri sai ya ga Umar da ita, sai ya ce: “Lallai ni, ban aikata zuwa gare ka domin ka daura ta ba, babu mai daura ta sai wanda ba ya da wani rabo a Lahira. Na aika maka ita ce domin ka sayar ka yi amfani da kudinta.”
557. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Nafi’u daga Alkasim dan Muhammad daga A’isha Uwar Muminai (Allah Ya yarda da ita) cewa, lallai ta ba shi labari cewa: Hakika ita, ta sayi wani majingini mai hotanni. Lokacin da Manzon Allah (SAW) ya gan shi (majingini) sai ya tsaya a kofar daki bai shigo ba. Sai na fahimci alamar kyama a fuskarsa, sai na ce: “Ya Manzon Allah! Ina tuba zuwa ga Allah, kuma ina tuba zuwa ga ManzonSa (SAW), wani laifi na yi? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce me ya samu wannan majingini? Na ce, “Na saye shi ne, domin ka rika zama a kanta, kuma kana jingina da ita.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Lallai ma’abuta wadannan hotuna za a azabtar da su Ranar kiyama, sai a rika ce musu: “Ku rayar da abin da kuka kaga (halitta).” Kuma ya ce, “Lallai gidan da hotunan nan suke cikinsa mala’iku ba su shigarsa.”
Babi na Arba’in da Biyu: Mai kaya shi ke da hakkin sanya farashin kaya:
558. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Abdul Waris ya ba mu labari daga Aby Tayyah daga Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “kabilar Bani Najjar ku sanya min farashin (kudin) gonakinku alhali akwai russasun gine-gine a cikinsu da dabinai, (wannan ya nuna mai kaya shi ke sanya farashi).”
Babi na Arba’in da Uku: Nawa ne gwargwadon lokacin da mutum ke da zabin ciniki?
559. An karbo daga Sadakat ya ce: “Abdulwahab ya ba mu labari, ya ce, Na ji Yahya ya ce, “Na ji Nafi’u daga Umar (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce: “Hakika masu ciniki biyu suna da zabi a tsakaninsu cikin cinikinsu matukar ba su rabu ba. Ko kuma ciniki bisa yarjejeniya (zabi).” Nafi’u ya ce, “dan Umar ya kasance idan zai sayi wani abin da ya ba ya sha’awa sai ya yi saurin rabuwa da mai shi saboda tsoron kada ya canja ra’ayi.”
Babi na Araba’in: Labarin mai yin kaho:
554. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Humaid daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi),…