✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babbar Sallah: Jihohi 6 na fuskantar barazanar COVID-19

Abuja da jihohin Kano da Kaduna da wasu shida za su kasance cikin shiri.

Gwamnatin Tarayya ta sanya jihohi shida a cikin shirin ko-ta-kwana a wani yunkuri na hana yaduwar cutar COVID-19 a yayin da al’ummar Musulmi suke shirin bukukuwan Babbar Sallah.

Kwamitin yaki da cutar na kasa ne ya sanar da hakan a yammacin Asabar tare da shawartar jihohin da su gudanar da sallolin idi a fili, su takaita tarukan jama’a, su kuma dakatar da shagulgula da hawan sallah.

Shugabanta kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce jihohin Kano da Kaduna da Legas da Filato da Oyo da Ribas da kuma Birnin Tarayya na fuskantar barazanar bazuwar cutar wadda a halin yanzu ake fadi-tashin yakar samfurinta na Delta.

Boss Mustapha ya bayyana cewa “Kwamitin ya sanya jihohin shida da Birnin Tarayya a shirin ko-ta-kwana a matsayin wani bangare na matakan kariya daga yaduwar cutar a karo na uku.”

Ya ce saboda haka, “Ya kamata duk jihohin su inganta yanayin shirinsu kuma su ci gaba da aiwatar da duk wasu matakai da aka tsara.

“Wadannan matakan suna da mahimmanci yayin da muka fara ganin alamun farko na masu kamuwa da cutar a Najeriya”.

Kakakinsa, Willy Bassey ya ce “gargadin” yana nuna cewa ya kamata jihohi su “yi amfani da dukkannin matakan kariyar COVID-19” tare da kara “yin gwaji, ganowa, magani da kuma killace wadanda suka kamu.”

A makon jiya ne NCDC ta ce ta gano wani nau’in kwayar cutar ta Delta mai saurin yaduwa, tare da sanya jami’ai a cikin shirin ko-ta-kwana game da yaduwar cutar.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) ta ce zuwa ranar Asabar, mutum kusan 169,000 sun kamu da cutar da kuma mutuwar 2,126.