Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta sanar da cewar mataimakiyar shugabanta, Fatma Samoura mace ta farko da ta samu wannan matsayi a hukumar, za ta yi murabus.
A cikin wata sanarwa, Samoura ta ce za ta yi murabus a karshen shekara, saboda tana son karin lokaci na kasancewa da iyalinta.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya jinjinawa ’yar kasar Senegal din a matsayin mai kwazo da biyayya.
Infantino ya ce jajircewarta da nuna sha’awa don kawo canji ya kasance abin burgewa.
Kazalika Samoura ta kasance Babbar Sakatariyar Hukumar FIFA ta farko wadda ba daga Turai ba.
Ta ce ta yi niyyar sanar da wannan matakin sauka daga mukamin nata a lokacin taron kwamitin FIFA a mako mai zuwa, amma sai ta dage sanarwar bayan da ta samu labarin rade-radi game da matsayinta.
Har yanzu dai ba a sanar da wanda zai gaje ta ba.