Jami’an Tsaro a Jihar Sakkwato, sun kama babban mai yi wa Bello Turji safarar makamai, mai suna Hamza Suruddubu.
Rahotanni sun bayyana cewar ana zarginsa da yi wa wasu maharan safarar makamai a jihar.
- An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB
- Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida
Wata majiya, ta shaida wa Zagazola Makama cewa Suruddubu ɗan yankin Gabashin Sakkwato ne, kuma ya daɗe yana safarar makamai daga jihar Zamfara zuwa sansanonin ‘yan ta’adda a Gabashin Sakkwato.
“Shi ne babban mai yi wa ƙasurguman ’yan bindiga irin su Bello Turji, Boka, da Halilu Buzu safarar makamai,” in ji majiyar.
Bincike, ya nuna cewa ba makamai kawai Suruddubu ke safara ba, har da wasu kayayyakin buƙata kamar abinci da babura domin taimaka wa ’yan ta’adda a yankin.
“Har ila yau akwai rahotannin da ke nuna cewa wasu jami’an tsaro a ƙananan hukumomin Shinkafi da Isa na da hannu a safarar waɗannan makamai,” in ji majiyar.
Shugabannin al’umma da masana tsaro sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike a kan Suruddubu.
Sun buƙaci a yi binciken don gano yadda ake safarar makamai tsakanin Isa da Sabon Birni.