Aminiya; mene ne mafufofin kafa wannan kungiya?
Mun fara tunanin kafa wannan kungiya ne a shekarar 2003. Wato a lokacin da aka fara samun ci gaba ta bangaren sadarwa a nan Najeriya musamman yanar gizo.
A lokacin akwai kafofin watsa labarai na kasashen waje kamar BBC Hausa da Muryar Amurka da Sashin Hausa na Jamus da Rediyo China suka fara bada dama ga masu sauraronsu, su rika tura wasiku da ra’ayoyi ana karantawa. A lokacin muna turawa ana karantawa muna jin mutane daga jihohi kamar ni daga Jihar Katsina da Zaidu Bala daga Jihar Kebbi da Saleh Shehu Ashaka daga Jos da Ali Jauro daga Kano da dai sauransu.
Daga nan muka fara kokari har Allah Ya taimakemu a cikin shekarar 2008 muka kafa wannan kungiya muka sanya mata sunan Muryar Talaka. A shekarar 2010 ne muka fara yin babban taron wannan kungiya. Mun yi zaben shugabannin wannan kungiya a shekarar 2013 a Katsina.
Manufar wannan kungiya ita ce a yi amfani da kafofin yada labarai kamar gidajen rediyo da jaridu na cikin gida da waje a dauki kukan talaka, a fada wa duniya da shugabanni a matakan kananan hukumomi da jihohi da tarayya baki daya. Saboda haka an kafa wannan kungiya ne domin habaka muradun talaka da kare hakkinsa ta hanyar kafafen yada labarai. Don haka zaka ga dukkan ayyukan wannan kungiya ya ta ‘allaka ne ga kafofin yada labarai da jaridu. Kuma muna shirya tarurrukan karawa juna sani da wayar da kan al’umma.
Bayan haka akwai aikace-aikace na jin kai da muke yi misali kamar taimakawa marayu da kai ziyara gidajen yari don fitar da fursunoni da ziyartar asibitoti don tallafawa marasa lafiya da dai sauransu. Wadannan su ne kadan daga cikin manufofin kafa wannan kungiya.
Aminiya; Kuna da membobi nawa a wannan kungiya tun kafa ta?
Ya zuwa yanzu muna da rassan wannan kungiya a jihohi 16 na Arewacin kasar nan. Haka kuma muna da wakilai a kudancin kasar nan da wasu kasahen waje kamar jamhuriyar Nijar da Chadi da Sudan da Saudiya da Amerika da Ingila. A takaice ya zuwa yanzu muna da mambobi sama da dubu 50 a ciki da wajen Najeriya.
Aminiya; Daga lokacin da kuka kafa wannan kungiya zuwa yanzu wadanne irin nasarori kake ganin kun samu?
Babbar nasarar da muka samu a wannan kungiya ita ce tun da muka kafa wannan kungiya har zuwa wannan lokaci muna rike da wannan kungiya kuma muna gudanar da ayyukanmu. Idan ka dubi yanayin yadda kungiyoyi suke tafiya a Najeriya, wannan ba karamar nasara bace. Domin zaka ga wata kungiyar ma ko shekara daya bata yi a raye sai kaga ta mutu.
Nasara ta biyu ita ce har zuwa yau wannan kungiya tana nan kanta a hade. Saboda shugabannin wannan kungiya suna yin komai bisa gaskiya da rikon amana . Abu na uku yau a Najeriya da duniya baki daya babu inda ba a san sunan wannan kungiya ta Muryar Talaka ba.
Wata babbar nasarar kuma da muka samu ita ce, wannan kungiya a kullum tana gwagwarmaya kan yadda talakan Najeriya zai sami yancin kansa. Wannan yasa shugabanni da yawa suna tafiya da wannan kungiya. A cikin gwagwarmayar da aka rika yi a Najeriya a yau muna da mutane daban daban da suke cikin gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi. Saboda ana tunanin duk dan kungiyar Muryar Talaka mutum ne mai gaskiya da adalci da rikon amana. A cikin irin mutanenmu da aka zabo aka saka a cikin gwamnatin tarayya akwai ministan matasa da wasanni Barista Solomon Dalung. Kowa ya san wannan mutum dan kungiyar Muryar Talaka ne kuma kowa ya san irin gwagwarmayar da ya yi ta kare hakkin talakawan Najeriya da kuma ganin an sami hadin kai a tsakanin mabiya addinai da kabilu. Wannan ne ya sanya shugaban kasa Muhammad Buhari ya dauko shi ya bashi mukamin minista a cikin wannan gwamnati.
Bayan haka akwai Bashir Ahmed mai taimakawa shugaban kasa Muhammad Buhari kan kafofin yada labarai na zamani shi ma dan wannan kungiya ne.
Haka idan muka koma ga jihohi mataimakin gwamnan Jihar Zamfara Malam Ibrahim Wakkala dan wannan kungiya ne. Muna da mutane da dama a cikin gwamnatoci jihohi musamman jihohin Arewacin kasar nan. Kuma muna da iyayen wannan kungiya masu hali, wadanda suke taimaka mana a kowanne lokaci. Don an ce Muryar Talaka ba wai ana nufin talauci bane. Ana nufin kungiya ce wadda take daukar bukatun talaka ta kai su inda ya kamata, domin a sami mas’hala.
Kuma mutane da dama suna zuwa su sami wannan kungiya su roki ta yi musu jagora don warware wasu matsaloli. Misali kamar a Jihar Zamfara wannan kungiya akwai mutane da yawa da suka sami matsaloli na rashin lafiya kamar yin tiyata a asibiti mun hada su da mutane sun taimaka masu. Akwai wasu mutane marayu a Sakkwato da aka so a cinyewa gona wannan kungiya ta taimaka wajen daukar lauyoyi muka tabbatar an yi adalci aka maido masu da gonarsu.
Haka kuma a kwanakin baya wannan kungiya ta shirya taron gangami a Jihar Katsina na bayar da magunguna kyauta. Mun shirya gasar karatun Alkura’ani mai girma a Katsina mun rabawa wadanda suka zama zakaru kyaututtuka a wajen gasar. Ga maganar wayar da kan talakawa. Wadannan su ne kadan daga cikin nasarorin da wannan kungiya ta samu.
Aminiya; Mene babban burinku?
Babban babban burinmu shi ne talakan Najeriya ya sami ‘yanci kuma Najeriya ta gyaru.