✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Baban Ramota ya ƙalubalanci Kannywood

Jarumin barkwanci da ke fitowa a matsayin Bayarabe, Baban Ramota ya ƙalubalanci masu shirya finafinan Kannywood da su riƙa tuntuɓar masana wurin samar da finafinansu.…

Jarumin barkwanci da ke fitowa a matsayin Bayarabe, Baban Ramota ya ƙalubalanci masu shirya finafinan Kannywood da su riƙa tuntuɓar masana wurin samar da finafinansu.

Muhammad Aƙilu, wanda aka fi sani da Baban Ramota ko Baban Mulika ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da Aminiya.

Ya ce masu shirya finafinai na da sun nemin ilimin abun yayin da na yanzu ke aiki da ka.