Wata Ba’amurkiya da ta kashe dan Najeriya ta shiga hannu a yayin da take kokarin tserewa daga Najeriya zuwa kasarta.
Bayan gano ana neman Ba’amurkiyar bisa zargin aikata kisa ne jami’an Hukumar Shige da Fice sun tsare ta a filin jirgi na Mohammed Murtala da ke Legas, a lokacin da take jiran jirgi don komawa kasarta.
Ana zargin matar da ofishin ’yan sandan filin jirgin ke tsare da ita da kashe wani dan Najeriya mai suna Adebayo Micheal Ayomide a otal din da ta sauka a unguwar Victoria Island da ke Legas.
Yunkurin Ba’amurkiya na sulalewa daga Najeriya ranar Litinin yayin da ake neman ta ya samu cikas ne saboda karewar wa’adin shaidarta ta gwajin cutar COVID-19 don haka dole sai ta jira.
Wakilinmu a Legas ya gano cewa wadda ake zargin ta shiga hannu ne a ranar Talata a dakin jiran matafiya na kamfanin Qatar Air inda aka tisa keyarta zuwa ofishin Hukumar Shige da Fice da ke filin jirgin.
Majiyarmu ta ce: “Jami’inmu tare da wani jami’in tsaron Hukumar Kula da Filayen Jirage (FAAN) ne suka kawo ta ofishinmu da misalin 12:30 na safiyar 9 ga Fabrairu, 2021 bisa zargin aikata kisa.”
Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sanda na filin jirgin, Oladimeji Oladosu amma ya tura shi zuwa ga Hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas.
Ya nemi jin ta bakin mai magana da yawun Rundunar, SP Olumuyiwa Adejobi amma ya ce masa sai ya samu karin bayani tukuna.