Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bai wa dan kasar Amurka Edward Snowden takardar shaidar zama dan kasar.
Mista Edward shi ne ya fallasa kutsen da Hukumar Leken Asiri ta kasar Amurka ta yi wa kasashe.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 12 a Taraba
- Ambaliyar ruwa ta mamaye hanyar Babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja
Wannan na zuwa ne bayan Ba’amurken ya yi kwarmaton bayanai, inda ya tsere daga kasar, kuma Rasha ta ba shi mafaka.
Shugaban ya ce, an sanya Edward Joseph Snowden da aka haifa a ranar 21 ga watan Yunin 1983 a cikin jerin sunayen sababbin ‘yan kasar Rasha, a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Washington da Moscow ta yi tsami saboda rikicin Ukraine.
Shi dai Snowden ya ce, a watan Nuwamban shekarar 2020 ya nemi izinin zama dan kasar Rasha, amma zai ci gaba da zama dan kasar Amurka.
Tsohon jami’in leken asirin Amurkan, wanda ya bayyana a shekarar 2013 cewa, Gwamnatin Amurka na yi wa ‘yan kasar ta Rasha leken asiri.
Bayan wannan fallasa sai ya koma zaman gudun hijira a Rasha.
Shekaru da dama da suka gabata Moscow ta sassauta tsauraran dokokinta na zama dan kasa don bai wa mutane damar rike fasfo na Rasha ba tare da wofantar da asalin kasashensu ba.
Lauyan Snowden Anatoly Kucherena ya shaida wa kamfanin dillancin labaran kasar Rasha RIA Novosti cewa, matarsa Lindsay Mills ita ma yanzu za ta nemi izinin zama ‘yar kasar Rasha kuma ‘yarsu ta riga ta mallaki fasfo na Rasha da aka haifa a kasar.
A makon da ya gabata ne Putin ya ba da sanarwar tattara mutanen Rasha don ba da gudummawar sojoji a yakin da kasarsa ke yi da Ukraine, amma lauyansa Kucherena ya ce ba za a kira Snowden ya yi aiki ba ganin cewa ba shi da kwarewa a vangaren aikin soja.
Kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov ya shaida wa kamfanonin dillancin labarai cewa, Snowden ya samu takardar zama dan kasar Rasha ne sakamakon bukatarsa da ya mika.