✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Ba zan sauka daga mulki ba har sai na kawo karshen matsalar tsaro’

Ba na fatan sauka daga mulkin kasar nan a matsayin jagoran da ya gaza.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi kasar gabanin ya sauka daga kujerar mulki.

Shugaban Kasar ya ce yana fatan ba zai sauka daga mulkin kasar nan ba a 2023 a matsayin jagoran da ya gaza.

Buhari ya yi furucin hakan ne yayin zaman Majalisar Tsaro da aka gudanar ranar Alhamis a Fadarsa ta Villa da ke Abuja.

A yayin zaman ne Shugaba Buhari ya karbi rahoto daga Ministan Tsaro, Bashir Salihi Magashi da sauran Manyan Hafsoshin Tsaro game da yanayin tsaron kasar.

Babban Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaron Kasa, Birgediya Janar Babagana Monguno mai ritaya ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai a Fadar Gwamnatin Najeriya.

A cewar Monguno, Shugaba Buhari ya yi farin ciki da rahoton da ya karba dangane da yanayin tsaron kasar laakari da nasarorin da aka samu a bayan nan na murkushe yan taadda a sassa daban-daban na kasar.

Har wa yau, Monguno ya ce Shugaba Buhari ya bayyana aniyyarsa ta kasancewar cikin shiri a koda yaushe domin gudanar da sauye-sauye da yi wa tsarin tsaron kasar garambawul idan bukatar hakan ta taso musamman a fagen yaki da ta’addanci a Arewa maso gabashin kasar.

Aminiya ta ruwaito cewa, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyema da takwaransa na Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola na cikin wadanda suka halarci taron.

Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da Shugaban Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ma sun halarci taron, wanda ke zuwa bayan dubban mayaka da kwamandojin kungiyar Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga sojojin Najeriya a Jihar Borno.

A baya-bayan nan sojojin Najeriya sun ragargaji maboyar mayakan Boko Haram a yankin Dajin Sambisa da Dutsen Mandara da ke Jihar ta Borno da kuma maboyar ’yan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma.

Wata sanarwar da rundunar sojin kasar ta fitar a baya kan mika wuyan ’yan Boko Haram din, ta ce mayakan na neman a yafe musu.

Sun alakanta mika wuyar da ragargazar da sojojin ke yi musu da kuma rabuwar kai tsakanin bangarorin kungiyar da kuma rashin lafiya da yunwa da ta addabi tsoffin mayakan.

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta shiga cikin rudani ne tun bayan da shugabanta, Abubakar Shekau, ya yi kunar bakin wake bayan ’yan kungiyar ISWAP mai mubaya’a ga kungiyar ISIS sun ritsa shi da wasu mataimakansa domin su yi wa ISWAP mubaya’a.