✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan kaddamar da shari’a ba idan na zama shugaban Najeriya- Yariman Bakura

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, kana Sanata a karo na uku a Najeriya kuma yake yunkurin tsayawa takarar shugaban kasa a…

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, kana Sanata a karo na uku a Najeriya kuma yake yunkurin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023, ya bayyana cewa indan ya zama shugaban kasa ba zai kaddamar da shari’ar musulunci a Najeriya ba.

Sanata Yarima, ya shaida hakan ne a tattaunawarsa da jaridar Aminiya a gidansa da ke Abuja, ya ce ya kaddamar da shari’ar musulumci a jihar Zamfara bisa tsarin dokar kasa.

“Na mika kudirin ga majalisa wadanda suka tabbatar da shi ya zama doka, kasancewar jihar kaso mafi yawanta Musulmai ne kuma nayi hakan ne bayan na tuntubi Kiristoci mazauna jihar inda na shaida masu cewa, tsari ne da ya shafi musulmi kawai.” In ji shi.