Tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Harkar Tsaro, Sambo Dasuki ya fada wa babbar kotun Abuja cewa ba zai iya tuna lokacin da ya bayar da ummarnin a tura wa tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Olisa Metuh Naira miliyan 400.
Dasuki wanda kotun ta umarci ya shiga kewayen bayar da shaida na kotun don ya bayar da bahasi kan shari’ar Metuh ya ce ba zai iya tuna wata mu’amala ba har sai ya kai ga duba takardunsa.
Da lauyan Metuh, babban lauyan Najeriya Emeka Etiaba ya tambaye shi kan abin da ya sani dangane da Naira miliyan 400 da ofishinsa ya tura wa kamfanin Destra, sai Dasuki ya ce ya san Metuh a matsayin mai magana da yawun jam’iyyar PDP amma ba zai iya bayar da gamshashshiyar shaida ba.