✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba zan halarci taron rantsar da Biden ba – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ba zai halarci bikin rantsar da wanda zai gaje shi a matsayin Shugaban kasar ba, Joe Biden.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ba zai halarci bikin rantsar da wanda zai gaje shi a matsayin Shugaban kasar ba, Joe Biden.

Trump dai a lokutan da dama ya sha zargin an tafka magudin da ya ba Mista Biden na jam’iyyar Democrat nasara kuma ko a makon nan sai da magoya bayansa suka yi zanga-zanga tare da yin ta’asa a ginin majalisar kasar.

Ya sanar da matsayin nasa ne wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma’a, duk da yake bai yi cikakken bayani a kan dalilinsa na kin halartar ba.

“Ga dukkan wadanda suke ta tambaya ta, ba zan je taron rantsar da sabon Shugaban Kasa ranar 20 ga watan Janairu ba,” inji Shugaba Trump.

Trump dai ya sha kaye ne bayan ya gaza kai bantensa a karo na biyu a hannun Mista Biden a zaben da aka yi a watan Nuwamban 2020.