✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba zan daina fim saboda aure ba —Rahama Sadau

Tana mamakin yadda ake son mata su yi wasu ayyuka da sana'o'i amma ake kyamar fim

Tauraruwa a masana’artar fim ta Kannywood, Rahama Sadau ta bayyana cewa ba za ta daina yin fim saboda aure ba.

Rahama Sadau ta bayyana haka ne a lokacin tattaunar da take yi da masu bin ta a kafar sada zumunta ta Twitter mai taken #AskRahama inda wani ya tambaye ta ko shin za ta iya barin yin fim saboda aure.

“Saboda me zan daina fim don na yi aure? Shin yin fim ba sana’a ba ce?”

Tauraruwa Rahama Sadau ta ce ta yi mamakin yadda mata suke taka rawa a wasu fannoni na ayyuka amma sai a yi ta kyarar matan da ke yin fim.

Ta ce, “Me ya sa ba a ganin matsala idan mace tana yin wata sana’a ko aiki a wata ma’aikata, amma banda harkar fim? misali aikin jarida.”

Ta kara da cewa wane dalili ne ya sa ake samun matan aure a wasu masana’antu da dama, amma ba a son hakan a masana’artar fim?

%d bloggers like this: