Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ko da ya fadi zaben fidda gwani, ba zai bar PDP ba.
Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ofishin Jam’iyyar PDP a lokacin da ya je karbi fom din tsayawa takara a sakatariyar ofishin a Abuja.
“Yarjejeniya a fitar dad an takara shi ya fi kyau, amma wasu ‘yan takara sun fi son zaben fidda gwani. Idan shugabanni jam’iyya suka ce ga wanda suke so, zan yi biyayya.”