Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya bayyana cewar za a ci gaba da sayar litar man fetur a kan N162 a cikin watan Yuli, kafin cimma yarjejeniya da kungiyar kwadago.
Wannan na zuwa daidai lokacin da farashin gangar danyen mai a duniya ya kai $74.72 a ranar Talata.
- Babu hannunmu a tarwatsa zanga-zangar daliban Gidan Waya – Gwamnatin Kaduna
- Hatsarin mota ya lakume rayukan ’yan Najeriya 2,233 a wata 4
Da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin na ARISE a ranar Talata, Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya ce za a ci gaba da sayar da litar fetur a kan N162 kafin samun tsayayyen farashi.
A cewarsa, ya kamata ya yi a rika sayar da litar man a kan N256 duba da farashinsa a kasuwar duniya, amma Gwamnatin Tarayya ta yanke hukuncin ci gaba da sayar da shi a kan farashinsa na yanzu kafin cimma matsaya da NLC.
Kazalika, ya ce Shugaba Buhari, ya ba da umarnin saukaka farashin ta yadda ’yan Najeriya za su iya saya ba tare da sun takura ba.
Kyari ya bayyana cewa za a bayar da aikin gyaran matatun Warri da na Kaduna a watan Yuli.
Ya ce za a yi hakan ne don tabbatar da cewa gyaran nasu ya tafi daidai da aikin matatar Fatakwal da tuni aka ba da shi.