✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zafin kai kuka fi mu ba —Matawalle ga ’yan Kudu

Ya ce idan lokaci ya yi za su gane cewa Arewa ba kanwar lasa ba ce

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya ce ’yan Kudancin Najeriya su kwana da sanin cewa ba zafin kai suka fi ’yan Arewa ba, don sun ga ’yan Arewan na kai zuciya nesa kan abin da ake yi wa ’yan uwansu a can.

Matawalle ya ce kawaicin da ake yi wa ’yan Kudu ba tsoro ba ne, amma idan suka ci gaba da nuna cewa ba sa son zaman lafiya, to Arewa daidai da su take, domin ba zafin kai aka fi ta ba, son zaman lafiya ne ke sa take kai zuciya nesa.

Gwamnan ya kuma caccaki shugabannin Kudu kan yadda suke dora laifin ta’adin da ake yi wa ’yan Arewa a yankunansu a kan su ’yan Arewan.

A cewarsa “Mun ga irin barna da kisan da aka yi wa ’yan Arewa a Kasuwar Sasha. Bayan rayukan da aka salwantar, an lalata kadarori na biliyoyin Naira, amma wasu Shugabannin Kudu-maso-Yamma suke neman a yi watsi da batun.

“Wadansunsu ma goyon bayan ta’asar suke yi; babu kunya, har nema suke yi su dora laifin a kan mutanen Arewan da abin ya ritsa da su,” inji Gwamnan.

Yana wadannan kakkausan kalaman ne a cikin sanarwar da ya fitar domin nuna bacin rai game da yadda ake kashe ’yan Arewa tare da barnata dukioyinsu a kan abin da bai taka kara ya karya ba.

Sanarwar ta jaddada cewa muddin tura ta kai bango a yadda ake kai wa ’yan Arewa a Kudu hari, to ita ma Arewa ba za ta raga musu ba.

“Matukar ba za a kare rayuka da dukiyoyin ’yan Arewa dake zaune a Kudu a kuma rungume su a mutunta su ba, to ’yan Kudu da ke Arewa kada su yi zaton za su samu kariya, saboda Arewa na da duk abin da ake bukata na yin fuskantar kowace irin farmaki ko kiyayya,” inji shi.

Gwamnan Zamfaran ya kuma caccaki shugabannin Arewa kan yadda suke kin fitowa su yi magana da babbar murya su nuna fushinsu kan irin cin kashin da ake yi wa jama’arsu mazauna Kudu.

“Duk da irin abubuwan da ake yi wa ’yan Arewa, musamman  a Kudu-maso-Yamma da Kudu-maso Gabas, Shugabannin Arewa da ya kamata su tashi su yi magana, sun ki cewa uffan sabanin takwarorinsu na Kudu da suke fitowa su yi babatu ko da kuwa ’yan uwansu ne ke da laifi,” inji shi.

Cikakken jawabin Gwamna Matawalle

Dole A Dakatar da Kashe Yan Arewa a Kudu –  Gwamna Matawalle
– Cin mutuncin Shugaba Buhari a Landan bai dace ba

Ya zama dole a matsayina na Gwamna kuma mai kishin Arewa na yi magana akan abubuwan da suke faruwa a kasar nan.

Wannan ba magana ce ta siyasa ba. Lokaci ya yi da za mu fada wa kanmu gaskiya domin dauwamar zaman lafiya da ci gaban kasarmu, da kuma kare Najeriya daga afka wa tashin hankalin da wasu bata-gari ke kokarin yi.

Duba da yadda muke yin siyasa a kasar nan, za ayi tsammanin jawabi irin wannan daga Gwamna ko wani shugaba na jam’iyar APC zai fito, ba ni ba cikakken dan jam’iyar adawa ta PDP.

Na yanke shawarar yin wannan jawabi ne saboda kishin Najeriya tare da neman wanzar da zaman lafiya da cigaban Arewa.

Abubuwa da dama, marasa dadi, na faruwa ga Arewa da kuma mutanen Arewa. A kullum ana kashe ’yan Arewa, ana lalata dukiyoyinsu a wasu sassa na Kudancin kasar nan duk da kokarin da shugabannin Arewa ke yi na kwantar da hankalin mutanensu, da kare mutunci da rayuka, da dukiyoyin ’yan Kudancin Najeriya mazauna Arewa.

Duk da irin mawuyacin halin da ’yan Arewa suka samu kansu musamman a Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas, shugabanni da manyan mutane ’yan Arewa sun yi shiru.

Maimakon su mara wa yankinsu da jama’arsu baya sun yi tsit, sabanin mutanen Kudu wanda ke kare mutanensu koda kuwa ba su da gaskiya.

Shiru da shugabanin Arewa suka yi duk da tsangwamar mutanensu da ake yi domin tabbatar da zaman lafiya a kasa ba tsoro ba ne.

Ko wacce alu’mma za ta iya dukkan abin da ya kamata domin kare kanta in hakan ya zama dole.

In dai ba za a tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Arewa a Kudancin Najeriya ba, to kada a yi tsammanin Arewa za ta kare ’yan Kudu mazauna Arewa.

A kwanakin baya an kashe ’yan Arewa, aka kona dukiyoyinsu a Kasuwar Sasa. An tafka asara mai dimbin yawa, amma shuwagabannin Yarabawa ba su yi komai ba a kai, sai ma kare miyagun da suka yi wannan ta’asa da suka yi. Wasun su ma cewa suka yi laifin mutanen Arewa ne.

Biyo bayan kisan da aka yi wa ’yan Arewa a jihar Imo ranar Lahadin da ta gabata, ya zama dole a yi Allah-wadai da kisan gilla da kiyayyar da ake nuna wa ’yan Arewa a Kudancin kasar nan.

Ba zamu kara yarda a kashe mana mutane ba. Ko wanne dan Najeriya yana da damar yin kasuwanci a ko ina.

’Yan Kudu na da tarin dukiya a Arewa fiye da yadda ’yan Arewa ke da ita a Kudancin kasar nan, amma babu wanda yake musu barazana.

A koyaushe muna kokarin wanzar da zaman lafiya. In a ka yi duba na tsanaki a kan rahotannin farmakin da ake kaiwa ’yan Arewa a Kudancin Najeriya, za a gane masu son zaman lafiya, da wadanda burinsu ta da hankali to tunzura mutanensu.

Kowa ya san su waye ’yan iskan da suke kai farmaki (kan ’yan Arewa), da wadanda ke daukar nauyinsu. Mun san masu yada kiyayya da masu tada tarzoma.

Amma abun takaici sun hana Gwamnatin Tarayya daukar wani mataki a kan haka; gwamnati ta zuba musu ido suna cin karensu babu babbaka.

Najeriya kasa daya ce. Duk wanda ba ya son ci gaba da zamanta a dunkule, yana da damar kalubalantar tsarin mulkin kasar, ko kuma ya tattara ya bar kasar, amma ba ya rika yi wa wasu ’yan kasa barazana ba.

A matsayina na Gwamnan jam’iyar PDP, ban yarda da siyasa ta ko-a-mutu-ko-ai-rai ba. Neman mukami ba za ya hana mu fadin gaskiya ba, ko goyon bayan mutanenmu yayin da ake takalar su da fada.

A matsayina na dan Arewa, ina Allah wadai da yadda wasu suke cin mutuncin Shugaba Buhari kuma suna nuna kiyayya a fili ga Arewacin Najeriya da sunan zanga-zanga.

Duk irin korafin da suke da shi, ba hujja bane abin da suka yi. Abin da suka yi tsagoron jahilci ne, kuma batanci ne ga Shugaban Kasa. Wannan na tabbatar da irin kiyayyar da ake nunawa Arewa. Zagin Shugaban Kasa ba shi ne hanyar isar da korafi ba.

Zagin Shugaban Kasa kaskanci ne da nuna kiyayya, kuma shiri ne na Kudancin Najeriya, domin kuwa mun san wadanda suka yi zagin da masu daukar nauyinsu.

Doka ta amince da zanga-zanga ta lumana, amma amfani da zanga-zanga don cin mutuncin Shugaban Kasa, iyalinsa ko iyayensa (kamar yadda ya faru a Landan) abin takaici ne, abin Allah-wadarai ne.

Da Buhari dan Kudu ne, tabbas ba za zu yi masa haka ba. Makasudin yin zanga-zangar shi ne muzanta Shugaban Kasa.

Wannan ya sa idan aka duba za a ga cewa masu zanga-zangar ’yan tsiraru ne, in aka yi la’akari da yawan ’yan Najeriya mazauna birnin Landan.

Idan Arewa na son cigabanta, ya zama dole ta kare kanta, kuma dole shugabanni su jajirce wajen kare Arewa kamar, ko fiye ma da yadda ’yan Kudu su keyi, a duk lokacin da aka taba musu mutum ko wani abu.

Kada mu ji kunyar kare mutuncinmu kamar yadda abokan zamanmu ke yi.

Amma kada mu kare laifukanmu (kamar yadda suke yi).

Najeriya kasarmu ce gaba daya. Dole kowane dan Najeriya ya yi kokarin dauwamar da zaman lafiya.

Dole a rika jan mutanenmu a Arewa a jika, kamar yadda mu ke jan mutanen Kudu a nan Arewa.

Idan kuma hakan ba za ta samu ba, to mu ba za mu lamunci irin abun da ake yi wa ’yan Arewa a sassan yankin Kudu a ’yan watannin da suka gabata ba.

Sa hannu:
Alhaji Dr. Bello Mohammed,
(Matawallen Maradun),
Mai girma Gwamnan Jihar Zamfara.