✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba za mu taba manta Ali Kwara ba

Najeriya ba za ta manta da gudunmuwar Ali Kwara wajen farautar ’yan fashi ba.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya juyayin rasuwar shahararran mafarauci mai yaki da barayi, Alhaji Ali Kwara.

Buhari ya ce Najeriya ba za ta taba mantawa da gudunmuwar Ali Kwara na yakar ’yan ta’adda da ’fashi da ke boyewa a dazuka ba.

“A madadin gwamnati da daukacin ’yan Najeriya, muna ta’aziyya ga jama’a da Gwamnatin Jihar Bauchi bisa mutuwar hazikin dan kishin kasa da ya sadaukar da rayuwarsa kacokan wurin tabbatar da doka da kuma yakar masu aikata muggan laifuka”, injin sakon ta’aziyyar.

Sakon da ya aike ta bakin kakakinsa, Garba Shehu ya ce al’umma da dama na alhinin rasuwar mai yaki da ’yan ta’addan.

Ya ce, “Mun yaba da kokarinsa kuma yawancinn mutanen da Ali Kwara ya kama sun shiryu, wasu kuma suna sauraron hukuncin shari’a. Allah Ya yi masa sakayya da Aljannah”.

Ali Kwara, a cewarsa, ya sadukar da rayuwarsa na wurin yakar miyagun ’yan ta’adda a yankin jihohi 19 da ke Arewacin Najeriya.

Garba Shehu ya ce bayan rasuwar Ali Kwara a Abuja a jinyar da gwamnati ta dauki nauyi a ranar Alhamis, gwamnati ta tanadi jirgin da ya kai gawarsa zuwa filin jirgin sama na Dutse, Jihar Jigawa, dagan nan kuma aka dangana da ita zuwa mahaifarsa da Azare, Jihar Bauchi don yi masa sallah.