Kasar Birtaniya ta yi wata sabuwar doka da za ta haramta wa dalibai ’yan Najeriya da ma wasu ’yan kasashen daga zuwa kasar karatu da iyalansu, daga watan Janairun badi.
Kafar yada labarai ta Sky News ta rawaito cewa hakan na cikin wani mataki da kasar take shirin dauka na rage yawan daliban da sue zuwa kasar karatu.
- HOTUNA: Yadda Buhari ya kaddamar da sabon ginin hedikwatar Hukumar Kwastam
- Buhari ya kaddamar da Titin Kano-Kaduna da Gadar Neja II
Yanzu haka dai masu karatu a kasar daga wasu kasashen sun kusa miliyan daya.
A karkashin sabuwar dokar dai, kasar za ta haramta wa daliban izinin sauyawa daga damar yin karatu zuwa ta yin aiki a kasar lokacin da suke karatun don kaucewa daina amfani da ita ta inda ba ta dace ba.
Kafar ta Sky News ta kuma ce za a fara hukunta jami’an ilimin da suke amfani da izinin shiga kasar ta wajen wani dalili, a maimakon karatu kawai.
Dokar za ta fara aiki ne daga farkon watan Janairun 2024, kuma za ta ba sabbin daliban da ke neman gurbin karatu a kasar kafin lokacin su fara shiri.
A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimin kasar da aka wallafa ranar Talata, Sakataren Ilimin Kasar, Suella Braverman, ya ce sun fuskacina ana samun karin yawan wadanda suke fakewa da sunan karatu suna kawo iyansu kasar.