✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kaddamar da Titin Kano-Kaduna da Gadar Neja II

A rana guda Buhari ya kaddamar da manyan ayyuka guda bakwai kwana 6 kafin ya bar mulki

Kwana shida kafin saukarsa daga mulki, shugaban kasa mai barin gado Muhammadu Buhari ya kaddamar babbar titin Kano zuwa Kaduna da kuma katafariyar Gadar Neja ta II da wasu manyan ayyukan raya kasa guda shida.

A ranar Talata Buhari ya laharci taron kaddamar da sabon ginin Hedikwatar Hukumar Kwastam ta Najeriya da ke Abuja, sannan ya kaddamar da sauran manyan ayyukan guda shida ta intanet a sassan Najeriya.

Ya kaddamar da manyan ayyukan ne a yayin da yake jagorantar wani zama na musamman na Majalisar Zartarwa ta Tarayya a Fadar Shugaban kasa.

Fitattu da ayyukan da Buhari ya kaddamar su ne titin Kano zuwa Kaduna mai nisan kilomita 200, wanda gwamnatinsa ta gyara da kuma gadar Neja ta biyu, wadda aka fara shekara 16 da suka gabata, ya kuma sanya mata sunansa.

Su biyun na daga cikin manyan ayyuka bakwai da Gwamnatin Buhari ta kammala na da suka hada da gine-ginen Sakatariyar Gwamnatin Tarayya guda uku da manyan gadoji uku da kuma aikin titin.

Gine-ginen Sakatariyar Gwamnatin Tarayya sun hada wadda ke Awka, hedikwatar Jihar Anambra, wanda aka fara a watan Disamban 2011.

Sauran gadojin sun hada da ta Loko zuwa Oweto, wadda ta ratsa Kogin Binuwai ta hade jihohin Binuwai da Nasarawa; da kuma Gadar Ikom da ke Jihar Kuros Riba.

Na biyu shi ne wanda ke Gusau a Jihar Zamfara kammala a watan Nuwamban 2022, sai wadda ke Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa, wadda aka bayar a 2011, aka kammala a watan Nuwamban 2022.

A watan Fabrairun 2023 Buhari ya kaddamar da ginin Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Lafia, hedikwatar Jihar Nasarawa.