Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya gargadi shugabannin kwadago cewa rundunar ba za ta lamunci tashin hankali yayin zanga-zangar da za a yi ranar Laraba ba.
Aminiya ta rawaito cewa kungiyar kwadagon ta bayyana cewa za ta tsunduma yajin aiki a fadin kasar nan tare da yin zanga-zangar neman dawo da farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan.
- Yariman Gombe ya riga mu gidan gaskiya
- Mambobinmu sun fara sayar da gidajen mansu saboda rashin ciniki – Kungiyar dillalan mai
Sai dai shugaban ’yan sandan ya bayyana damuwarsa kan abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan dangane da shirin gudanar da zanga-zangar da kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC da TUC suka shirya.
Da yake zantawa da manema labarai a hedkwatar rundunar da ke Abuja, Kakakin rundunar na kasa, Olumuyiwa Adejobi, ya bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su tabbatar da zaman lafiya yayin zanga-zangar.
Ya ce ya kamata shugabannin kungiyoyin su tabbatar da cewa sun hana bata-gari shiga cikin zanga-zangar.
A cewarsa, Sufeton ya amince da korafe-korafen da kungiyoyin kwadago suka gabatar da kuma muhimman batutuwa don magance matsaloli.
Adejobi ya ce, “Hanyar zaman lafiya da hadin kai na da matukar muhimmanci wajen samun mafita mai ma’ana da kuma hana duk wani nau’i na tashin hankali ko kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a.
“Rundunar ’Yan Sandan Najeriya na nanata kudurinta na tabbatar da tsaron dukkan ’yan kasa a lokacin gudanar da zanga-zangar da aka shirya.
“Duk da haka, an sake tabbatar da cewa duk wani yunkuri na yin ta’adi ko yin amfani da lamarin wajen haddasa fitina ba za mu lamunce shi ba.
“Rundunar ’yan sanda ba za ta amince da duk wani abu da ke kawo barazana ga zaman lafiya a kasarmu ba.
“Bisa la’akari da kalubalen da zanga-zangar ka iya haifarwa, rundunar ’yan sandan Najeriya ta shirya tsaf domin tura duk wani abu da ake bukata don tabbatar da doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa.
“Saboda haka, Babban Sufeton ’Yan Sandan ya yi kira ga dukkan jami’an rundunar da su kasance masu lura da nuna kwarewa yayin aikinsu,” in ji shi.