✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu kwace gasar cin kofin kwallon kafa na duniya daga Rasha ko katar ba -Hukumar FIFA

A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta bayar da sanarwar cewa ba ta da hurumin da za…

A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta bayar da sanarwar cewa ba ta da hurumin da za ta kwace daukar nauyin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya daga kasashen Rasha da kuma na katar. Rasha ce za ta dauki nauyin gasar a shekarar 2018 yayin da katar kuma za ta dauki nauyin na shekarar 2022.

Hukumar FIFA ta yi wannan bayani ne jim kadan bayan wata jarida da ake wallafa wa a Suwizilan mai suna Domerico Scala ta yi hasashen watakila a kwace gasar daga kasashen biyu muddin aka same su da laifin bayar da toshiyar baki a lokacin da shugabannin hukumar suka gudanar da zaben kasashen da za su dauki nauyin gasar a baya.
Idan za a tuna, dambarwar cin hanci da rashawa dai ta sarke hukumar FIFA a ’yan kwanakin nan, al’amarin da ya sa jami’an tsaron Amurka suka kama 14 daga cikin jiga-jigan Hukumar a bisa zarginsu da cin hanci da rashawa. Hakan ta sa shugaban Hukumar Mista Sepp Blatter ya bayar da sanarwar sauka daga mukaminsa nan da karshen shekarar nan da muke ciki.
Hakan ce kuma ta sa wasu suke zargin akwai yiwuwar kasashen Rasha da katar sun bayar da cin hanci kafin a ba su damar daukar nauyin gasar cin kofin dunjiya a kasashensu wanda za a yi a shekarar 2018 da kuma ta 2022 bi da bi.
Sai dai Hukumar FIFA ta ce magangagun da ake yadawa na kasashen Rasha da katar sun bayar da cin hanci kafin a ba su damar ba gaskiya ba ne, har sai an kammala bincike. “Zargi ba gaskiya ba ne har sai an tabbatar da hakan”, kamar yadda FIFA ta nuna a sanarwar da ta fitar.