Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da kungiyar ma’aikata (TUC) sun ce ba za su amince da N100,000 a matsayin mafi karancin albashi a kasar ba.
Kungiyoyin sun bayyana hakan ne bayan da suka yi watsi da shirin gwamnatin kasar na biyan Naira 62,000 a matsayin mafi karancin albashin.
Wannan sabuwar dambarwar ta taso ne bayan a ranar Litinin kwamitin da gwamnatin ta kafa ka lamarin ya mika wa fadar shugaban kasar rahotonsa bayan shafe watanni biyar yana zama.
Za a iya tuna cewa a makon jiya NLC da kungiyoyin da ke karkashinta suka dakatar da yakin aikin da suka fara bayan wakilan gwamnati da ake tattaunawa da su sun ba ta tabbacin samun kari a kan albashin Naira 60,000 da gwamnatin ya gabatar musu a lokacin zaman.
A lokacin dai NLC ta dage a kan cewa mafi karancin albashin Naira 494 ne za ta amince da shi.
Gwamnatin ta kira zaman da aka cimma waccan matsaya ne bayan yajin aikin ya gurgunta harkokin kasar.
To sai dai NLC ta bayyana cewa ba idan karin da za a yi daga N60,000 bai taka kara ya karya ba, to za ta koma yajin aiki.
Zuwa ranar Juma’a dai, Naira 2,000 gwamnatin ta kara a kan N60,000 din bayan an ci gaba da tattaunawan kwamitin, wanda ya hada da wakilan kamfanoni masu zaman kansu.
Ita kuma NLC ta sauko daga N494,000 zuwa N250,000.
Babu batun yajin aiki —Ajaero
Amma da yake jawabi a ranar Litinin, Shugaban NLC na Ƙasa, Kwamared Joe Ajaero, ya ce a halin yanzu kungiyar ba za ta koma yajin aiki ko zanga-zanga kan lamarin ba.
Ajaero ya shaida wa wani taron zababbun ’yan jarida a birnin Geneva na kasar Switzerland, inda yake halartar babban taron kungiyar kwadago ta duniya cewa, kwamitin tattaunawa kan mafi karancin albashin ya mika rahotonsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ajaero ya shaida wa manema labarai cewa NLC ba za ta tafi yajin aiki ko ta dauki wani mataki a ranar Talata ba, sai ta jira ta ji matsayar da Shugaba Tinubu ya dauka kan kudin albashin da kwamitin ya gabatar masa.
Ya ce, “Kwamitin ya mika rahotonsa wanda bangaren gwamnati da masu kamfanoni suka ba da N62,000, kungiyar kwadago kuma ta tsaya a kam N250,000. Muna jiran matakin da shugaban kasa zai dauka.
“Daga nan shugabanninmu za su zauna su tattauna kan abin da shugaban kasa ya ce.
“Ba za mu kira yajin aiki ba, sai mun jira shugaban kasa mun ji abin da yanke kan albashin.
“Dalili shi ne a lokacin tsohon shugaban kasa Buhari, Naira 27,000 rahoton kwamitin ya gabatar masa, amma sai shugaban kasa ya kara zuwa N30,000.
“Saboda haka muna da kyakkyawan fata cewa shugaban kasa zai yi abin da ya dace, musamman ganin cewa ya bayyana cewa tazarar da ke tsakanin N62,000 da N250,000 mai yawan gaske ce,” in ji Ajaero.
Gwamnoni sun soki karin albashin N62,000
Shugaban na NLC ya kuma soki Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) bisa adawar da ta nuna kan karin albashin da gwamnati da kamfanoni suka yi zuwa N62,000.
Ya ce, “Ya za su ba za su iya biya ba? Ba su da hujjar neman a rabe albashi tsakanin gwamnati, saboda ai nasu ba rabewa aka yi ba.
“Ai alabshin gwamnonin da jihohinsu ke bayar da gudummawar biliyoyi a asusun tarayya daya ne da alabshin gwamnonin jihohin da ba sa taimakawa da komai a asusun tarayya kuma harajin jihohinsu ba taka kara ya karya ba.
“Sai su fara neman a sanya wannan bambanci a albashi da sauran hakkokinsu — gwargwadon gudummuwar jihohinsu ga asusun tarayya.
“Idan sun cw ba za su iya ba, ya aka yi Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo yake biyan mafi karancin albashin Naira 70,000?
“Irinsa ne gwamnonin da ya kamata a yi koyi da su ba raggaye ba,” a cewar Kwamred Ajaero.
Aminiya ta ruwaito mataimakin sakataren kungiyar TUC, Chris Onyeka a ranar Litinin na cewa, kungiyar idan gwamnati da Majalisar Dokoki ta Kasa ba su y abin da ya kamata kan mafi karancin albashin ba, kungiyoyin za su sake zama a ranar Talata su yanke shawara kan komawa yajinkungiyoyin za su sake zama a ranar Talata su yanke shawara kan komawa yajin aikin.
Mika wa Tinubu rahoton
Segun Imohiosen, sakataren yada labaran kwamitin mafi karancin albashi mai mambobi 37 karkashin jagorancin Alhaji Bukar Goni, ya tabbatar da mika rahoton a ranar Litinin ga Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akumeh.
Ya ce za mika rahoton a hukumance ga Tinubu da zarar shugabannin kungiyar kwadago sun dawo daga taron kungiyar kwadago ta duniya da suka je halarta a Geneva.
A ranar 30 ga Janairu 2024 Shugaba ya kafa kwamitin ya kuma ɗora masa alhakin ɓullo da sabon mafi karancin albashi na kasa ga ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni.
Duk da cewa kokarinmu na samun ganin abin da ke cikin rahoton bai kai ga nasara ba, ana sa ran idan komai ya tafi daidai, daga bisani Tinubu zai rubuta tare da gabatar da dokar shugaban kasa kan karin albashin ga majalisa.
Idan ta amince za ta dawo masa da dokar domin ya rattaba hannu kan sabuwar dokar albashin.
Me kananan hukumomi ke so?
Shugaban Kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON), Aminu Muazu-Maifata, ya ce duk da cewa suna goyon bayan karin alabshin, kudaden da suke samu daga Tarayya ba zai iya biyan albashi sannan su yi manyan ayyuka ba.
Muazu-Maifata, ya yi kira da a kara kason kananan hukumomi daga asusun tarayya ya haura kashi 18% domin su samu damar sauke nauyin da ke wuyansu.
A yanke albashin gwamnoni
Ana iya tuna cewa NLC ta yi wa kungiyar raddi cewa karuwar kudaden shigan asusun tarayya daya Naira biliyan 700 zuwa tiriliyan 1.2 ya kara wa gwamnoni, amma suka bar talakwa cikin fatara.
A hirar da wakilinmu suka yi da ma’aikatan gwamnati kan dambarwar mafi karancin albashin, ma’aikatan gwamnati sun bukaci a zaftare albashin gwamnoni da masu mukaman siyasa da suka nada domin a biya sabon mafi karancin albashin.