✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu gaza a wajen gudanar da aikinmu ba Inji ACG Victor Gbemudu

Hukumar kwastan ta kasa  ta ce rudanin da ya barke tsakaninta da mutanen garin Badagry, wanda har ya yi musabbabin mutuwar  daya daga  jami’anta mai…

Mataimakin shugaban  kwastam na kasa mai kula  da  shiyyar A ACG Victor Gbemudu yana sa hannu a rajistar ta’aziyyar John MotojehiHukumar kwastan ta kasa  ta ce rudanin da ya barke tsakaninta da mutanen garin Badagry, wanda har ya yi musabbabin mutuwar  daya daga  jami’anta mai suna  John Motojehi ba  zai sa  ta gaza a gudanar da ayyukanta ba.
Mataimakin shugaban hukumar mai  kula  da  shiyyar  A, Mista  bictor  Gbemuda ne ya yi wannan kalamin sa’ilin da  yake  wa  manema  labarai  jawabi  bayan  ya  wakilci shugaban kwastan din  wajen  ta’aziyyar mamacin, biyo  bayan  tashin  hankalin  da  ya  barke  tsakanin  wasu ’yan  simoga  da  jami’an kwastan  da ke  bakin iyakar Najeriya  da Jamhuriyar  Benin.
Ya ce  hukumar  tana  jimamin rasuwar jami’in wanda ’yan  fasa  kwaurin suka yi  wa  taron  dangi  ne har daga  bisani suka kona  motar da yake ciki sa’ilin da  yake kan hanyarsa ta zuwa bakin  aiki.
Mista Gbemuda ya ce an kame wasu  daga  cikin  wadanda  ake  tuhuma  da  aikata  wannan danyen  aikin,  kuma  za a ci  gaba da bincike har sai an gano wadanda ke da  hannu  ciki kuma hukumar ba za ta kyale  ba,  sai  ta ga  an yi  adalci, domin  haka  ya  zame  darasi  ga  masu  tunanin  aikata  irin haka.
Dangane da  ko akwai  wani  tsari  da  hukumar  ta yi  ko kuma  za ta  yi  domin  ganin  haka  bai  sake  faruwa  ba, mataimakin shugaban ya ce  za su  kara  inganta  dangantakarsu  ne da mutanen da suke zaune tare da su domin su kara fahimtar juna,  kuma batun yin sako-sako da aikinsu bai ma taso ba, sai ma dai su kara kaimi.
Mista bictor  ya ce  zuwansa  gidan  marigayin  wata  manuniya  ce  ga  sauran  jami’an  cewa  wanda  duk ke  aikinsa  kuma  wani  abu  ya  same  shi  ko da  ba  mutuwa  ba ne  ya san yana  da  goyon  bayan  hukumar, don haka ya yi kira  ga  jami’an na kwastan  duk  inda  suke  cikin Najeriya  su kara kaimi wajen tafiyr  da  aikinsu.
Daga karshe ya ce  hukumar  za ta dauki  nauyin  karatun ’ya’yan  marigayin har  zuwa  jami’a kuma  a kowace  makaranta  suke  son  zuwa,  kuma ta yi alkawarin  daukan dawainiyar  iyalinsa.