Majalisar Dattawa ta sanar cewa za ta gudanar da bincike kan zargin danne hakki da Alkalan Kotun Koli ke yi wa tsohon Alkalin Alkalai na Najeriya, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad wanda ya yi murabus a kwanan nan.
Majalisar ta ce duk da dai Mai Shari’a Tanko ya yi murabus daga mukaminsa, hakan ba zai hana ta gudanar da bincike kan zargin da alkalan ke yi a kansa ba.
- Buhari zai kai ziyara kasar Portugal
- Ba za mu yi wa zabin ‘yan Najeriya katsa-landan ba a 2023 – INEC
Wannan na zuwa ne biyo bayan korafin da Shugaban Kwamitin Shari’a da Hakkin Dan Adam na Majlisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ya yi yayin zaman Majalisar a ranar Talata.
Sanata Bamidele ya bijiro da batun ne dangane da bukatar gudanar da bincike kan zargin da alkalan suka yi, yana mai cewa hakan zai kawo karshen dambarwar da ta kunno kai a fannin shari’ar kasar.
Kafin wannan lokaci, alkalan Kotun Kolin sun rubuta wa Mai Shari’a Muhammad takarda inda suka sanar da shi a hukumanci yadda yanayin aikinsu ya tabarbare a karkashin jagorancinsa.
Rashin motocin aiki da rashin muhalli da tsadar lantarki da kuma rashin intanet da sauransu, na daga cikin kalubalan da alkalan suka ce suna fuskanta a wajen aiki.
Ana tsaka da wannan rudani ne Mai Shari’a Muhammad ya rubuta takardar sauka daga mukaminsa, inda ya kafa hujja da dalili na rashin lafiya.
Yanzu dai ‘yan Najeriya sun zuba wa Majalisar Dattawan ido da kuma dakon sakamakon binciken da ta ce za ta gudanar game da zarge-zargen da alkalan Kotun Koli suka yi.