Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sa hannu kan dokar kara albashin alkalai da ninki uku.
Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harokin Majalisa Basheer Lado, ya bayyana cewa a ranar Talata shugaban kasar ya sanya hannu kan dokar karin albashi alkalai da kashi 300%
A watan Jun ne Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da kudurin dokarin karin albashin alkalai da kashi 300%, wanda shugaban kasa ya aike mata.
Sanata Lado ya bayyana rattaba hannu kan kudirin da shugaban kasar ya yi a matsayin wani gagarumin nasara da kuma ke nuna jajircewarsa wajen kyautata rayuwar ma’aikatan Najeriya.
- Tinubu zai tafi kasar Equatorial Guinea ziyarar aiki
- Mutane na tona gidan tururuwa don neman abinci a Borno —Ma’aikaciya
Lado ya kuma bukaci alkalai a kasar da su kara himma wajen ganin an tabbatar da adalci da kuma gaggawa.