Gwamnan Filato Simon Lalong ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta bari jihar ta sake fadawa cikin rikici ba.
A ziyararsa ga wuraren da rikicin zanga-zangar #EndSARS ya shafa a kananan hukumomin Jos ta Arewa, da Jos ta Kudu ranar Laraba, gwamnan ya ce ba zai lamunci faruwar hakan a jihar ba.
Lalong ya yi takaicin abin da ya kira yadda masara kishi suka so su yi amfani da zanga-zangar don cimma manufarsu ta wargaza jihar.
Sai dai ya yaba da irin hadin kan da al’ummar jihar suka bayar wajen bin dokar hana fita ta awa 24 da aka kafa a jihar.
A jawabinsa, ya ce nan gaba gwamnati za ta sanar da mataki na gaba kan wannan dokar bayan jami’an tsaro sun yi nazarin halin da ake ciki.
A lokacin ziyarar, Lalong ya je kasuwar Terminus da titin Ahmadu Bello da sauran wuraren kasuwancin da rikici ya shafa a garin Jos, da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa.
Kuma ya ziyarci wuraren da aka yi kone-kone a hanyar Gyero da ke garin Bukur, Karamar Hukumar Jos ta Kudu.