Masarautun Katsina da Daura a Jihar Katsina sun dage gudanar da Hawan Sallar da aka saba yi a duk shekara.
Masarautun sun dakatar da hawan a bana ne bisa la’akari da yanayin tsaro, musamman batun ’yan bindiga da kuma cutar COVID-19.
- Yadda aka ceto masu Sallar Tahajjud da aka yi garkuwa da su
- An ceto matafiya 13 daga hannun masu garkuwa
Sanarwar mai dauke da sa hannun Sakataren Masarautar Katsina, Bello Mamman Ifo ta ce, “Sarkin Katsina Dokta Abdulmumini Kabir ya dauki shawarwarin da masu ruwa da tsaki a kan dakatar da hawan.
“Sai dai za a je a yi sallar idi, inda za a yi addu’o’i na musamman don samun zaman lafiya da rokon Allah Ya kawo wa jihar da ma kasa karshen matsaloli, musamman na tsaro da suka addabi jama’a.”
Shi ma Maimartaba Sarkin Daura, Dokta Farouk Umar Farouk ya sanar da dage hawan sallar bisa ga wadancan dalilai.
Sarkin na Daura, wadda ita ce mahaifar Shugaba Buhari, ya umarci hakimai da dagattai da su yi addu’o’in samun zaman lafiya daga yankunan da suke.