Ministan Lafiya a Najeriya Dokta Osagie Ehanire ya ce gwamnati ba za ta tilasta wa ma’aikatan lafiya su yi aikin dakile cutar coronavirus a kasar ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito ce wa ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da kwamitin yaki da cutar ke gabatar da jawabinsa a ranar Alhamis a birnin Abuja inda ya ce gwamnati tana aiki tukuru saboda samar da kayayyakin kariya.
Dokta Ehanire ya bukaci duk wani ma’aikacin lafiya da ba zai jure aikin ba da ya nuna kansa saboda babu wanda gwamnati za ta tilastawa sannan ya bukaci wadanda aka baiwa horo a kan yaki da cututtuka masu yaduwa da su kara azama.
“Ya kamata ma’aikatan lafiyar su san cewa babu wanda za a tilastawa ya yi aikin.
“Wadanda suke tunanin ba za su iya ba, suna da damar bayyana hakan, sai a maye gurnbinsu”, inji shi.
- Coronavirus: A karon farko mutum sama da 200 sun kamu a Najeriya
- Coronavirus: Karin mutum 12 sun warke a Legas
Ministan ya kara da cewa a halin yanzu dakunan gwaje-gwaje 15 ne a fadin kasar kuma suna iya gwajin mutane 2,500 a kowane wuni.
“Karin yaduwar cutar ya na nunawa a alkaluman da muke samu na wadanda suka harbu, hakan babbar barazana ce kuma ya kamata al’umma ta dauki wannan abu da muhimmanci ta hanyar kare kai”.
Zuwa karfe 11.50 na daren Alhamis dai mutane 1.932 aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya inda 319 suka warke kana 58 suka rasa rayukansu.